Yau Ne Za A Fara Jigilar Fasinjojin Jiragen Sama A Najeriya

0
464

Rahoton Z A Sada

A yau ne ranar Laraba 8 ga watan Yuli ne za a fara zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida a Najeriya.

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ta a uwitmakon da ya gabata.

Hadi Sirika ya ce za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama daga Abuja babban birnin kasar zuwa Legas daga ranar Laraba 8 ga watan Yulin da muke ciki, Kano da Fatakwal da Owerri da Maiduguri za su koma aiki daga ranar 11 ga watan Yulin.

Sauran filayen jiragen sama kuma za a buɗe su don fara jigilar fasinja daga ranar 15 ga watan Yuni.

Ga dai jerin dokokin da hukumar kula da filayen jiragen sama na kasar ta fitar.

Matakan hawa jirgin sama

Ma’aikatan filin jirgi za su jagoranci fasinjoji don tabbatar da an bi wadannan dokokin.

 • Dole fasinjoji su sanya takunkumi kafin su shiga filin jirgi
 • Dokokin dawo da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya
 • A wajen shiga jirgi, kamfanonin jiragen za su diga man kashe kwayoyin cuta a hannun kowane fasinja kafin su shiga jirgi
 • Bayan shinge, duk inda fasinjoji za su je, da ya hada da wajen tantancewa ko kuma wajen jira kafin shiga jirgi, akwai alamu da za su nuna yadda tsarin zaman zai kasance
 • Za a saka shinge mai shara-shara a wajen da kamfanonin jirage suke tantance mutane domin kariya
 • Hukumomin filin jirgi za su zana alama a kasa domin nunawa fasinjoji wajen tsayawa yayin da suke bin layin shiga filin jirgi
 • Ku wanke hannunku sannan ku yi amfani da man kashe kwayoyin cuta a kai a kai
 • Hukumomi za su ringa gwada zafin jikin fasinjoji
 • Ba za a bar masu rakiya da suke zuwa da manyan mutane su shiga dakin jira kafin tashin jirgi ba, fasinjoji ne kawai za su shiga
 • Ana shawartar masu daukar fasinjoji su ci gaba da zama a motocinsu har sai fasnjojin sun fito waje
 • Ana shawartar fasinjoji su je filin jirgi sa’a uku gabanin tashin jirgi saboda sabbin matakan kariya daga kamuwa da cutar korona
 • Ana fatan fasinjoji za su kiyaye ka’idar nisantar juna yayin da suke shiga motar da za ta kai su wajen shiga jirgi
 • Guji taba abubuwa a filin jirgi ba gaira ba dalili
 • Ba za a bar mutanen da ba tafiya za su yi su shiga gining tantance mataifya ba
 • Bayar da tazarar kafa shida (2m) tsakaninka da sauran fasinjoji a koyaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here