Mun Hana Barayi Sakewa A Karamar Hukumar Lere-Kwamandan Vigilent

0
430

Isah Ahmed Daga Jos

KWAMANDAN rundunar kungiyar ‘yan sintiri ta Vigilent Service ta Jihar Kaduna  reshen Karamar Hukumar Lere, Yahaya Isma’il ya bayyana cewa rundunarsu ta hana barayi da sauran masu aikata miyagun laifaffuka sakewa a Karamar Hukumar. Kwamanda Yahaya Isma’il ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce daga lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufa’i ya  kaddamar da wannan runduna a Jihar Kaduna shekaru 5 da suka gabata,  sun sami gagarumar nasara  a Karamar Hukumar Lere, wajen magance aikata miyagun laifaffuka.

Ya ce sun kama barayin babura da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifaffuka  da dama, sun mika wa ‘yan sanda, don mika su ga kotu.

Ya ce ko a ‘yan kwanakin nan, sun yi nasarar kama wasu barayin babura mutum uku, kuma   sun mika su ga ‘yan sanda.

 Kwamandan ya yi  godiya ga Mai Martaba Sarkin Saminaka kan goyan bayan da yake ba su wajen magance matsalolin tsaron da suke tasowa a yankin.

Ya ce Sarkin Saminaka yana ba su goyan baya, don kama irin yaran da suke wasa da babura a lokacin bukukuwa a yankin.

Ya yaba wa ga gwamnatin Jihar Kaduna, kan yadda ta kuduri aniyar tallafa wa ‘yan wannan kungiya, ta hanyar daukarsu domin a je a ba su horo da kayan aiki.

Ya ce zuwa yanzu gwamnatin jihar ta Kaduna, tana raba takardun fom a dukkan kananan hukumomin jihar,  don ‘yan  kungiyar su cika a yi masu wannan tallafi.

Ya yaba wa shugaban karamar hukumar  da babban jami’in ‘yan sandan yankin da manyan sarakunan yankin,  kan goyan baya da hadin kan da suke ba su.

Ya yi  kira ga al’ummar  karamar hukumar, su ci gaba da taimaka masu  wajen kama masu laifi a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here