Isah Ahmed Daga Jos
FITACCEN malamin addinin musuluncin nan da ke zaune a garin Jos, kuma daraktan ilmi na kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Ikamatu Sunnah na kasa, rashen jihar Filato Sheikh Abubakar Imam Bala Gana ya kai ziyara gidajen marayu na al’ummar musulmi da kirista da ke garin Jos, tare da tallafa masu da kayayyakin abinci.
Kayayyakin abincin da ya tallafa masu, sun hada da katan katan na taliyar Indome da buhunan samonbita da man gyada da buhunan omo da kwai da dai sauransu.
Da yake jawabi a lokacin da ya isa gidan marayu na Sheikh Haris Salihu, Sheikh Abubakar Gana ya bayyana cewa ya kawo wannan ziyara ce, domin ya karfafa masu gwiwa tare da tallafa masu.
Ya ce halin da ake ciki a kasar nan, bai kamata a tsaya ana nuna banbance-banbancen kabila ko addini ba.
A nasa Sheikh Harisu Salihu ya yaba wa malamin kan wannan ziyara da ya kawo masu. Ya yi kira ga sauran malaman addini suyi koyi da wannan malami. Ya ce matukar malamai za su rika yin irin wannan za a sami kyakyawan hadin kai da zaman lafiya, a jihar Filato da Najeriya baki daya.
Da yake jawabi a lokacin da ya isa gidan marayu na A’isha Mana Ophenage home, Sheikh Abubakar Gana ya bayyana cewa kula da marayu yana daga cikin koyarwar addinin musulunci.
Ya ce ya kawo wannan ziyara ce a matsayinsa na malamin addinin musulunci, domin karfafa zaman lafiya a jahar Filato da Najeriya baki daya.
Ya ce lokacin nuna kiyayya da zubar jini da sunan adinni ya wuce a jihar Filato. Domin dukkan addinan musulunci da kirista suna koyar da zaman lafiya ne.
A nasu jabawan Shugabannin gidan mayarun na Aisha Mana Ophenage home, sun bayyana matukar farin cikinsu da wannan ziyara.
Suka ce wannan tallafi da malamin ya ba su, ya nuna cewa al’umar musulmi da kirista kansu ya fara haduwa a jihar Filato. Daga nan sun nuna wa Malamin hanyoyin da gidan marayun yake samu kudaden shiga, da suka hada da gonakin da suke noma da wuraren kiwon kifi, da wajen koyan sana’a.