An Gano Hannun El-Rufai, Fayemi da Amaechi A Rikicin APC Na Ondo

0
334
Daga Usman Nasidi.
JAM’IYYAR APC reshen jihar Ondo ta zargi gwamnoni biyu da wani minista daya da sa hannu a rikicin jam’iyyar da ke aukuwar a jihar.
Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ondo, Henry Olatuja, ya zargi Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi da takwaransa na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi akan hura wutar rikicin jam’iyyar da ke balbali a jihar.
Olatuna ya ce goma daga cikin ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar na iya kin fitowa zaben fidda gwani da za a yi a ranar 20 ga watan Yuli.
Ya ce hakan za ta kasance ne idan kwamitin rikon kwarya na shugabancin jam’iyyar a matakin kasa suka nace cewa lallai sai an yi amfani da wakilai a zaben fidda gwani a jihar.
A baya rahotanni sun bayyana cewa a jiya Laraba ne aka tantance Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Gwamnan na cikin ‘yan jam’iyyar APC 12 da ke hankoron samun tikitin tsayawa takara a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba na 2020.
A wani sako da gwamnan jihar ya wallafa kan shafinsa na Facebook, ya yabawa mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar dangane da tsarin tantancewar da suka tanada.
Ya rubuta cewa: ” Yanzu haka dai jam’iyyata ta @OfficialAPCNg ta kammala tantance ni. “Mambobin kwamitin sun kasance suna dubawa sosai, sun binciki duk wasu takardu tare da gabatar da tambayoyi. Na yi imanin cewa jam’iyyar ta tanadi tsari mai kyau.”
Kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa dai, ya amince da tsarin amfani da wakilai a madadin ‘yar tinke wajen fidda gwanin takarar gwamnan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here