Matar Da Ta Guntule Wa Mijinta Azzakari Ta Haifi ‘Da Namiji

0
527
Daga Usman Nasidi.
WATA mata Halima Ali, wacce ta yanke wa Mijinta, Aliyu Umar, al’aurarsa a jihar Taraba da samu karuwar ‘da namiji a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2020.
A rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Halima asibitin Jalingo ne daga ofishin ‘yan sanda ranar Laraba yayin da ta fara nakuda.
An tattaro cewa Halima da dan jinjirinta na cikin koshin lafiya kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da ita a kotu kan laifin azabtar da mutum da kuma kokarin kisa.
Yayin da aka bayyana Halima gaba manema labarai, ta ce ta yi nadamar abin da ta yi.
A ranar Talata, 30 ga Yuni, 2020, uwargidar Aliyu Umaru, Halima, ta guntule masa azzakari da wuka.
Yana kwance yanzu a asibiti cikin radadin jiki da zuciya a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe, inda aka kai sa bayan aukuwar hadarin.
A asibitin, an ga yadda Likitoci suka sanya masa na’ura na musamman domin taimaka masa wajen fitsari yayin da aka ajiye azzakarinsa da matar ta yanke gefe guda cikin leda.
A hirar da majiyarmu ta yi da shi, Aliyu Umar ya bayyana irin iftila’in ya shiga ciki.
Ya ce: “Ni dillalin Likitocin dabbobi ne. Ina sayar da magungunan dabbobi. shekaru na 42 kuma ina da mata biyu da yara biyu.”
“Ni mazaunin garin Tella ne a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba. An turo ni asibitin koyarwar tarayya Gombe ne daga FMC Taraba.”
“Bayan dawowa na daga aiki, na debi ruwa don yin wanka kuma na ci abincin da iyalina ta girka kuma na yi bacci. Daga baya wani mugun azaba ya tashe ni daga barci ina ihu.”
“Uwargidata ta yanke min ‘bura’. A lokaci aka sanar da makwabta. Ban sani ba (akwai yiwuwar) an sanya magani cikin abincin saboda yadda na yi bacci mai zurfi. Matata ta lalata min rayuwa kuma akwai takaici.”
Rahotanni sun nuna cewa Halima ta kasance cikin takun saka da mijinta da kishiyarta.
Dan’uwan Umaru, Malam Usman ya bayyana cewa yana gidansa cikin dare aka kira shi a waya cewa akwai matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here