‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Ƴan Gida Ɗaya Su 8 A Abuja

0
855
Daga Usman Nasidi.
WASU mutane dauke da bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan tsohon darektan hukumar kananan hukumomi, ACSC, Alhaji Attahiru Abdullahi Pandagi, da ke Agyana road, Abaji, suka sace ‘ƴa’ƴansa takwas.
Bincike ya tabbatar da cewa wadanda aka sace sun hada da Jibrin, 26; Bashir, 24; Jamilu 26; Abdullahi 24; Abdulrahman 25; Abubakar 23; Muazu 22 da Isah, 12.
Majiyarmu ta samu rahoton cewa ‘yan bindigan sun raba kansu kashi uku ne suka kai wasu hare-haren a lokaci guda a Angwar Sabon Tasha da wani mashaya da ke kallon ofishin FRSC a unguwar.
Mahaifiyin yaran, Alhaji Attahiru Abdullahi Pandagi yayin zantawa da majiyarmu ya ce wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun haura katanga yayin da wasu suka tare wasu hanyoyin shiga gidan.
Ya ce ‘yan bindigan sun shiga dakunan samari inda yaran ke barci sun taso keyarsu da bindiga duk da cewa ya ce ba ya gida a lokacin da abin ya faru.
Ya ce, “Daya daga cikinsu ya tambayi matata cewa ina Isah yake, hakan ke nuna alama cewa suna da dan leken asiri da ya taimaka musu da bayanai.”
An gano cewa wasu yan banga da ke gadin gidajen manyan maaikata a unguwar sunyi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen hakan yasa suka tsere daga unguwar.
Wani na kusa da shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce shugaban ya shiga matukar damuwa saboda harin hakan ya sa ya tafi Abuja ya shaida wa Minista abin da ya faru.
Ya ce, “Shugaban karamar hukuma ya damu sosai game da harin da masu garkuwa da mutane suka kawo, ya tafi Abuja domin ya sanar da minister abin da ya faru.”
Idan ba a manta ba, wasu ‘yan bindiga a farkon makon nan sun sace diyar wani jigo a jami’yyar APC, Mrs Hasiya Gimba Bako sun kuma nemi a biya su kudin fansa Naira Miliyan 2.
Da aka tuntube shi, Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manza ya tabbatar da sace yaran inda ya ce ana kokarin ganin an ceto wadanda abin ya faru da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here