An Kama Fasto Yana Lalata Da ‘Yarsa A Ogun, Da Wasu Masu Fyade A Akwa Ibom

0
340
Daga Usman Nasidi.
JAMI’AN ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kama wasu mutane biyar da ake zargin sun yi wa kananan yara fyade a cikin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Akwa Ibom, CSP Fredrick Nnudam ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba, 9 ga watan Yuli, 2020 a garin Uyo.
Jami’in tsaron ya yi hujja da sashe na 1(2) na dokar haramta ta’adi ga mutane na shekarar 2020 wanda ya kayyade hukuncin daurin rai da rai ga wanda aka samu da laifi a jihar.
‘Yan sandan jihar sun gargadi mutanen Akwa Ibom game da aikata fyade ko makamancin wadannan laifuffuka na lalata da kananan yara da karfi da yaji.
A dogon jawabin da rundunar ‘yan sandan ta fitar a bakin CSP Fredrick Nnudam, ta bayyana daya daga cikin wanda aka kama har da ‘dan acaba mai suna Daniel Tommy.
Tommy da ke zama a karamar hukumar Abak, ya yi lalata da wata mai shekara 16 da ya dauko a babur, bayan haka ya karbe mata wayar salula ta N17, 000 da kudi N50, 000.
An kuma cafke wani Joseph Ekeruke Inyang mai shekara 36 a karamar hukumar Ikot Ekpene wanda shi kuma ya bata wata ‘yar shekara 13 da ke masa aiki a gida.
Akwai Godwin Willie a Ikot Ubo, da ke garin Ikot Ekpene wanda ake zargi da laifin amfani da ‘yar cikinsa mai shekara 15 da haihuwa.
‘Yan sanda sun ce sun yi nasarar damke wani mutumi mai suna Nsisong Moses Asuquo, shi ma a garin Ikot Ekpene wanda aka samu ya yi wa ‘yar shekara 13 fyade a gidansa.
Ba a nan kawai abin ya tsaya, a wani rahoton, an kama wani fasto da ke cocin Christ Apostolic Church (CAC) a jihar Ogun wanda aka samu ya na kwanciyar da ‘yar da haifa.
Fasto Oluwakemi Oyebola ya rika yi wa ‘yarsa fyade har ya kai ta dauki ciki sau uku, inda a duka lokacin aka zubar da juna biyun. Faston ya ce ya afkawa tarkon shaidan ne.
A ranar Alhamis aka samu labarin cewa faston ya kasance ya na kwana da ‘yarsa mai suna Owode-Egbado tun a 2015 lokacin da mahaifiyarta ta rasu, a wancan lokaci ta na da shekara 19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here