Ka Ki Bayar Da Beli Ranar Juma’a Amma Kana so A Ba Da Belin Ka – Shehu Sani Ga Magu

0
263

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

TSOHON dan majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, ya sake caccakar dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu.

Tsohon Sanatan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli, inda ya wallafa cewa mayen shugabancin EFCC na ta dibar Magu.

Magu, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin cin hanci, na tsare tun a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Sani ya bayyana cewa mafi akasarin maza a gurbin mulki kan manta da cewar mulki mai shudewa ne kuma yana zuwa da illoli.

Ya ce “A duk lokacin da ka tunatar da masu mayen mulki cewa mulki mai karewa ne kuma yana zuwa da illoli, sai su ga kamar ba zai taba faruwa a kansu ba.”

Tsohon dan majalisar ya yi mamakin dalilin da ya sa Magu wanda ya gaza bayar da beli ranar Juma’a a lokuta da dama ke rokon kwamitin shugaban kasa da ya bashi beli a yanzu.

“Mutumin da ya ke kin bayar da beli a ranar Juma’a ne ke son a bashi beli a ranar Juma’a; yana son karban abunda shi ba zai iya bayarwa ba,” in ji shi.

Sani ya bayyana cewa fursunonin kurkuku basu girmama manyan mutane.

Abu na farko da fursunoni za su fada maka idan ka shiga kurkuku shine “kai mallam nan kurkuku ne, muna da namu shugabancin a nan, kada ka zo kana babban mutum a nan, idan baka so mu dagargaza ka a nan toh ka bi a sannu da kuma biyayya a nan, ka ji ko?” ya wallafa.

A gefe guda, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa dakataccen mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu ya rika sayarwa abokansa kadarorin da ya ke kwato wa.

A cewar tsohon gwamnan na jami’yyar PDP, cikin wadanda Magu ke sayarwa kadarorin na gwamnati har da wasu lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here