Zafin Ciwo Ya Sanya Wani Mai Tabin Hankali Burma Wa Cikinsa Wuka

0
399

 Isah Ahmed Daga Jos

AL’UMMAR da ke zaune a garin Doka da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, sun wayi gari da wani abin mamaki, a ranar talatar da ta gabata. A inda wani mai mutum mai tabin hankali mai suna Dayyabu Salisu, da ke zaune a garin ya burmawa cikinsa wuka, ya ciro hanjinsa yana ja saboda tsananin zafin ciwon zazzabin typod, da yake fama da shi.

Da take yi wa wakilinmu bayyanin yadda wannan al’amari ya faru, a wajen da take yiwa wannan bawan Allah jinya, a babban asibitin garin Saminaka. Kanwar wannan bawan Allah mai suna A’isha Salisu, ta bayyana cewa wannan yaya nata, ya yi fama da zazzabin typod ne har na tsawo sama da wata guda.

Ta ce ana ta magani amma bai sami sauki ba. Ta ce  saura kwana daya a kawo shi, wannan  asibiti na  Saminaka, domin a yi masa magani kan wannan zazzabin typod da yake damunsa.

Ta ce da yake kansa ba dai dai ba ne, yana zaune  da ya ji zafin ciwo ya dame shi, kawai sai dauki wuka ya yanka cikinsa, ya kama jawo hanjinsa.

Ta ce shi ne da yara da suka ganshi, sai  suka rugo da guda suka fadawa mutane ga abin da yake faruwa. Nan take   mutane suka rugo suka yi kukan kura suka rufe shi, aka rufe cikin nasa da zannuwa aka kwaso shi aka kawo shi, nan asibitin Saminaka,  aka yi masa aiki. Kuma yanzu ya sami sauki, bayan da aka yi masa wannan aiki.

Ta ce likita  ya tambaye shi, maye yasa ya yi haka? sai ya ce da likitan  zafin ciwo ne yasa ya yi haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here