Amitabh Bachcan Ya Harbu Da Cutar Korona

0
300

Mustapha Imrana Abdullahi

HUKUMAR kula da kiwon lafiya ta Jihar Maharashtra da ke kasar Indiya sun tabbatar da cewa fitaccen dan wasan fina Finai Amitabh Bachcan ya kamu da cutar Korona

Sakamakon gwajin cutar da aka fitar ranar Lahadi ya nuna cewa Aishwarya Rai Bachchan, tsohuwar sarauniyar kyau ta duniya, da ‘yarta Aaradhya, ‘yar shekara takwas sun kamu da cutar korona.

Mijinta Abhishek da surukinta Amitabh, dukkansu sun kamu da cutar ranar Asabar kuma an kai su asibiti.

An ce taurarin biyu maza sun nuna alamar kamuwa da cutar.
Abhishek Bachchan ya wallafa sakon Twitter cewa suna ci gaba da zama a asibiti “har sai abin da likitoci suka yanke shawara a kai”.

Aishwarya Bachchan, mai shekara 46, na cikin fitattun taurarin fina-finan Bollywood a India da kuma kasashen waje, inda ta fito a fina-finan kasar da na Amurka da dama.

Rahotanni sun ce Aishwarya da ‘yarta ba su nuna alamar kamuwa da cutar ba. Mijinta ya wallafa sakon Twitter da ke cewa za su killace kansu a gida.
Ranar Asabar Amitabh Bachchan ya shaida wa miliyoyin masu bibiyarsa a Twitter cewa ya kamu da Covid-19.

“Na kamu da cutar korona, an kai ni asibiti, an yi wa iyalai da ma’aikata gwaji, ana jiran sakamako,” a cewarsa.
Bachchan, mai shekara 77, ya fito a fina-finai fiye da 200 a cikin shekara fiye da hamsin.

Bachchan ya lashe kyautuka da dama tun da ya soma tashe a shekarun 1970
An kai shi da Abhishek, mai shekara 44, asibitin Nanavati da ke Mumbai ranar Asabar. Abhishek ya bayyana cewa suna dauke da kananan alamomin cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here