An Daure Wani Mutum Da Ya Yi Wa ‘Yan Sandan DSS Sojan Gona Shekara 12

0
245
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ibadan babban birnin Jihar Oyo ta yanke wa wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin jami’in hukumar DSS hukuncin shekara 12 a gidan yari.
Daga cikin laifukan da aka zargi Ademola Lawal da aikatawa akwai damfarar kuɗi naira miliyan 1.85 da sunan wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS.
Da take bayyana hukuncin, Mai Shari’a Patricia Ajoku ta ɗaure Ademola Lawal bisa hujjojin da aka gabatar mata sannan kuma mai laifin ya amsa abubuwan da ake zarginsa da su, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito
“Na aminta cewa mai laifin ya nuna nadama da kuma zummar zai sauya halinsa ta hanyar amfanar da al’umma,” in ji Patricia Ajoku.
“Duk da haka, an yanke wa Lawal hukuncin shekara biyu kan kowanne laifi guda shida da ake zarginsa da su domin ya zama darasi ga sauran jama’a.”
Sai dai mai shari’ar ta ce zai yi zaman gidan yarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here