Katsina / ‘Yan Bindiga: ‘Yara Sama Da 2000 Sun Zama Marayu A Batsari’

0
376

Rahoton Z A Sada

UBAN kasar Batsari da ke jihar Katsina yankin arewa maso yammacin Najeriya ya ce akwai daruruwan mata da aka bari da marayu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mazajensu.

Hakimin na Batsari, Sarkin Ruman Katsina, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ya shaida wa BBC cewa ba zai iya kiyasta adadin mutanen da aka kashe ba, amma  ya ce “mata kimanin 600 ne aka kashe mazajensu yayin da aka bar marayu sama da 2000.”

Kaburbura a BatsariHakkin mallakar hoto@RARIYA
Hakimin Batsari ya ce kusan a kullum sai an kashe mutum a yankinsa

Uban kasar Batsari da ke jihar Katsina yankin arewa maso yammacin Najeriya

Sannan ya ce kusan kashi daya cikin uku na mutanen masarautarsa sun zama ‘yan gudun hijira inda suka warwatsu a jihohi makwabta da sauran sassan Najeriya.

“Sun yi muna ta’adi sosai duk kasar ta fashe kuma babu ranar da ba kai hare-hare, kusan kullum sai an kashe mutum daya zuwa biyu,” inji Hakimin na Batsari.

Ya kara da cewa, baya ga asarar rayuka da dukiyoyin da lamarin ke haifarwa, ya kuma gurgunta harkokin noma da kiwo da kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki.

A cewarsa ‘yan bindigar sun yi ta’adi duk kasar ta fashe sun hana noma da kiwo – “A bara kashi 40 cikin dari ba su yi noma ba saboda duk wanda ya fita za a yi garkuwa da shi.”

Basaraken ya ce yankinsa na cikin wani matsanancin hali na matukar bukatar agajin gwamnati da masu hannu da shuni, duk da ya ce gwamnati na ciyar da mutanen da ke gudun hijira a wani sansani.

'Yan gudun hijira a BaratsariHakkin mallakar hoto@SALISU LAWAL FACEBOOK
‘Yan gudun hijira a harabar fadar Sarkin Ruman Katsina a Batsari

Hukumomi dai suna cewa suna daukar matakan shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin arewacin Najeriya.

Amma ‘Yan bindigar masu fashin daji sun tsawwala kai hare-haren duk da rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da sabon farmaki ƙarƙashin umarnin shugaban ƙasar na fatattakar ‘yan bindigar daga jiharsa.

Karuwar hare-haren na ‘yan bindiga da ake kai wa yankunan na Katsina ya haifar da zanga-zanga a watannin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here