Lantarki : Gwamna Ganduje Ya Yaba Wa Buhari

0
216

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNAN jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya yaba wa gwamnatin tarayya a kan kafa wata katafariyar tashar samar da wutar lantarki a karamar hukumar Bichi domin bunkasa samuwar wutar lantarki a jihar.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan sadarwa da hulda da jama’a Malam Aminu Yassar ya sanya wa hannu aka raba wa manema labarai.

Ganduje ya yi wannan yabon ne yayin da yake karbar bakuncin Shugaban Kamfanin rarraba wutar lantarki (TCN), Alhaji Sule AbdulAziz, wanda ya ziyarci  fadar gwamnatin Jihar Kano.

Kamar yadda Gidan Talabijin na kasa NTA ya ruwaito, Gwamnan ya ce wannan katafaren aiki zai kawo ci gaba da habbakar tattalin arziki a jihar bayan gushewar annobar korona.

Ganduje ya yi godiya ga shugaba Muhammadu Buhari da kuma Ministan Lantarki da suka jajirce a kan taimaka wa jihar wajen farfado da tattalin arzikinta, musamman ma bayan an gama da kalubalen cutar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here