Mutum 20 Sun Mutu Cikin Awa 24 A Saudiyya Sakamakon Cutar Korona

0
260

Rahoton Z A Sada

SAUDIYYA ta bayar da rahoton samun adadi mafi ƙaranci na waɗanda suke mutuwa kullum sakamakon cutar korona cikin mako biyu, inda mutum 20 suka rasu cikin awa 24 da suka gabata.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa an kuma samu mutum 2,852 da suka kamu da cutar, abin da ya sa jimillar adadin waɗanda suka kamu a ƙasar ya kai 235,111, a cewar ma’aikatar lafiya ranar Litinin.

Saudiyya

Saudiyya na samun mutum 30 zuwa 56 da ke mutuwa a kullum tsawon mako biyu da suka gabata, kamar yadda bayanai daga ma’aikatar lafiya suka nuna.

Yanzu haka jimillar mutanen da suka mutu sakamakon cutar sun kai 2,243 a Saudiyya.

A gefe guda kuma, adadin waɗanda suka warke daga cutar ya kai 169,842 bayan an samu ƙarin 2,704 da suka warke, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar, Dokta Muhammad Al-Abdel Ali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here