Rundunar Tsaro Ta NSDC Ta Yi Kokari Kan Kamo Wanda Ya Yi Wa ‘Yar Wata Uku Fyade

0
473

Isah Ahmed Daga Jos

SAKATAREN Kungiyar tallafa wa marayu ta Haske Support Foundation da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato. Kuma matashin nan da ya fara yada labarin yarinyar nan ‘yan wata uku da aka yi wa fyade a Jihar Nasarawa kwanakin baya, a kafafin sada zumunta na yanar gizo, Yusuf Salihu Namaska  ya yaba wa rundunar tsaro da kare al’umma ta kasa [NSDC] reshen Jihar Nasarawa. Karkashin jagorancin babban Kwamandan rundunar Dokta Muhammad Mahmud Gidado Fari,  kan kokarin da suka yi wajen damko mutumin da ya yi wa yarinyar ‘yar wata uku fyade. Yusuf Salihu Namaska ya yi wannan yabon ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce a matsayinsa na wanda ya fara yada labarin wannan yarinya, a kafofin sada zumunta gaskiya ya yi matukar farin ciki da wannan kokari da Kwamanda Muhammad Gidado Fari ya yi, tare da rundunarsa wajen kamo wannan mutum.

Har’ila yau ya ce Kwamandan wannan runduna daga zuwansa Jihar Nasarawa zuwa yanzu, ya yi kokari wajen kamo irin wadannan miyagun mutane da suke yi wa kananan yara fade, da sauran masu aikata miyagun laifaffuka a jihar.

Ya  ce babu shakka da sauran jami’an tsaro suna gudanar da ayyukansu kamar haka, da an sami nasarar magance matsalolin da suke faruwa kan harkokin tsaro, a kasar nan.

Ya yi kira ga gwamnati ta rika tsayawa wajen ganin ana yi wa masu fyade da sauran masu aikata miyagun laifaffuka,  hukunci a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here