Akwai Rufin Asiri A Kasuwancin Manja-Hamisu Mai Manja Saminaka

  0
  538
  Alhaji Hamisu Rabi'u Mai Manja Saminaka
  Isah Ahmed Daga Jos
  ALHAJI Hamisu Rabi’u Mai Manja Saminaka da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, wani mai kasuwancin Manja ne da ya yi fice   a yankin Saminaka da sauran yankunan da suke makotaka da wannan yanki.
  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara wannan kasuwanci na Manja shekaru 33 da suka gabata, da irin nasarorin da ya samu da kuma shawararsa ga matasa, kan mahimmancin kama sana’a. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
  A wane lokaci ka fara wannan kasuwanci na sayar da manja?
  Hamisu Mai Manja: Na fara kasuwancin Manja kamar shekara 33, da suka gabata. Kuma wani maigidana a garin Jos ne, ya fara bani   Manja doran daya ya ce naje na gwada, na dauko wannan Manja kan N300. Daga nan ina dauko duron 10, sai duron 20, ina kawowa nan garin Saminaka.
  Daga nan  sai na koma Kalaba, ina sayo wannan Manja ina kawowa  nan garin Saminaka. Ina nan ina cigaba da wannan kasuwanci, har ya zuwa wannan lokaci da muke ciki.
  A matsayinka na wanda ya dade yana kasuwancin  Manja, ya ya zaka kwatatan yadda wannan kasuwanci yake ada, da yanzu?
  Hamisu Mai Manja: Ada kasuwancin Manja yafi kwanciyar hankali, kuma kudade sun fi albarka. Amma yanzu abubuwa sun canza. Domin ada zaka sanya kudin ka N2,000 zuwa N3,000 kaje ka ciko mota da Manjan nan, amma yanzu Manja ya yi tsada. Akwai shekarar da sai da duron Manja, ya kai N150,000.
  A bayan sallar nan da ta gabata, mun sayo duron Manja kan kudi N60,000, amma a makonni  biyu da suka gabata, mun sayo duron Manja har N97,000.
   Abin da yake kawo tashin farashin Manja, shi ne a duk shekara yana irin wannan tashin farashi,  domin duk lokacin da aka ce damina ta sauka,  can wajen da muke sayo  Manja a kudanci, ana ruwa kamar da bakin kwarya. Don haka shiga dajinsu a wannan yanayi na damina, yana da wahala. Saboda haka a wannan lokaci, manja yake tsayawa.
  Idan ya tsaya su kuma  ‘yan kasuwa, sai su kara farashi, idan suka ga masu saye sun yi yawa. Dalilin da yasa Manja yake tashi ke nan, a irin wannan lokaci.
  Daga lokacin da ka fara wannan kasuwanci zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne ka samu?
  Hamisu Mai Manja: Gaskiya na sami nasarori da dama, domin an ci an sha an yi ayyuka na alheri an taimaki ‘yan uwa. Kuma ban san yawan adadin yara da rike ba, a wannan kasuwanci. Na kafa yara da dama, wasu   sun yi gidaje da iyali, sun zama masu zaman kansu duk a jikina a wannan yanki, har daga Zariya da Katsina da Kafanchan da yakin jihar Kano.
  Kuma na kafa kamfanina na yin Man gyada da Manja mai suna Guroshel Oil, duk da yanzu wannan kamfani, baya aiki saboda matsalar wutar lantarki.
  Kuma duk abin da ya taso na taimakawa al’umma muna yi. Yanzu a ‘yan kwanakin nan ma akwai wani aikin gayya da muka yi a hanyar unguwarmu ta Nasarawa,  daga babban masallacin Juma’a na Saminaka. Inda  gefe da gefen  hanyar duk ya cinye. Mun kawo bulo muka gina hanyar, sannan muka kawo kasa muka cike.
  Wadanne irin matsaloli ne ake samu a wannan kasuwanci na Manja?
  Hamisu Mai Manja: Gaskiya akwai matsaloli a wannan kasuwanci na Manja. Na farko wani lokaci  za a doro maka kaya daga kudu, bayan kasa kudi ka sayo, sai a kawo duk ka sami ruwa da tabo a ciki. Babu yadda zaka yi ka koma da shi, dole sai ka zauna ka tace shi, sannan ka sayarwa da mutane. Sannan matsala ta biyu ita ce su kuma ‘yan kasuwa, da yawa yawansu akwai mata da maza, da zasu zo su karbi kayan, tun da bashi ake rabawa ana taimakon al’umma. Idan ka baiwa wasu mutane bashin wannan kaya,  kan  kudi N8,000 jarka, sai suje su sayar N7,500 su biya bukatarsu. Kwana kadan sai kudin su karye masu.
  Wanne mahimmanci ne wannan kasuwanci na  Manja yake da shi?
  Hamisu Mai Manja: Gaskiya  wannan kasuwanci na Manja yana da matukar mahimmanci, domin kasuwanci ne wanda zaka ci, zaka sha kuma zaka taimaki al’umma. Idan har zaka yi saboda Allah, zaka ga biyan bukata. Kuma kasan komai sai da hakuri, kuma kasan mutanen mu na yanzu basu da hakuri. Gaskiya akwai rufin asiri, idan mutum ya yi hakuri kuma ya rike gaskiya. Yanzu kaga ni kamar yadda na fada maka, tun da farko shekara 33 ke nan ina wannan kasuwanci, amma kaga yaran yanzu kowa da ya kama kasuwanci, so yake yi nan take ya yi kudi.
  Wannan kira ne kake da shi zuwa ga matasa kan mahimmanci kama sana’a ko kasuwanci?
  Hamisu Mai Manja: Kirana ga matasa shi ne duk sana’ar da mutum zai yi, ya hada da hakuri kuma ya rike gaskiya. Kada mutum ya ce da zarar ya fara sana’a mutum ya ce, yana son ya zama wane nan take. Idan mutum yayi hakuri, yana tafiya a hankali, idan Allah ya nufa zai zama wani abu, zai zama idan kuma Allah zai rufawa masa asiri ne, a ciki yaci ya sha ya taimaki kansa da kansa, ya godewa Allah. Domin shi arziki na Allah ne. Don haka ina kira ga matasa su san wannan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here