Ba Mu Dauki Mataki Kan Auren Dan Malami Ba Don Babu Rahoton Karya Dokar Korona – Gwamnatin Kano

0
305

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN Kano ta shaida cewa, babu wanda ya kai korafin cewa mutane sun karya ka’idojin da aka gindaya don kauce wa kamuwa da korona a bikin dan ministan shari’a Abubakar Malami wanda aka gudanar a makon da ya gabata, shi ya sa ba su dauki mataki ba.

Hotunan bidiyo da aka rinka wallafawa a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda mutane cunkus ke ta rakashewa suna liki da kudi a bikin Abdulazeez Malami da Khadija Dambata, wanda hakan ya saba sharuddan da gwamnatin tarayya da ta jihar ta gindaya wa mutane don dakile yaduwar annobar korona.

Abdulazeez Malami and im wife Khadija DambattaHakkin mallakar hotoABBAVILLA PHOTOGRAPHY/FACEBOOK
Abdulazeez Malami da matarsa Khadija Dambatta

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya ce, bangaren shagalin bikin da gwamnatin Kano ta shirya a fadarta an bi umarnin bai wa juna tazara sosai.

”Kuma ce-ce-ku-ce da ake kan wannan biki da aka gudanar, ba mu samu rahoto ko guda da ke tabbatar da cewa mutane sun karya ka’idojin korona a wurin bikin ba, don haka ba mu da hujjar daukar mataki.”

”Kazalika batun bikin da muka dau nauyi a fadar gwamnatin Kano mun bi duk matakan kariya daga korona sai dai ba mu san abin da ya faru a wani wajen ba cikin shagulgulan bikin, hasalima babu wanda ke da hujjar cewa akwai wasu mutane da suka karya dokoki a bikin da aka gudanar a Kano.” Kalaman Muhammad Garba kenan.

Sai dai sabanin wadannan kalamai na kwamishinan, hoton da aka dauka a gidan gwamnatin Kano ya nuna yadda gwamnoni da sauran mutane suka cakudu wuri guda a hoto babu wata tazara tsakaninsu.

Minister of Justice Abubakar Malami with Kano govnor Abdullahi Ganduje and oda govnors for di weddingHakkin mallakar hotoBADARU MEDIA/FACEBOOK
Ministan shari’a Abubakar Malami da mai masaukin baki Gwamna Kano Abdullahi Gandujue da wasu Gwamnonin jihohi a wurin bikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here