Gwamnati Ta Sake Bude Makarantun Kasar Nan-Sheikh Jingir

0
293
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir
Isah Ahmed Daga Jos
SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake bude makarantun kasar nan da ta rufe, sakamakon annobar korona. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne, a lokacin da yake gabatar da wa’azi a masallacin Juma’a na ‘Yan taya, da ke garin Jos a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce sam bai kamata gwamnati ta sake shawarar da ta yi na sake bude makarantun kasar nan ba. Ya ce gaskiyar magana abin da  ma’aikatar ilmi ta taryya ta yi,  na canza shawarar sake bude makarantun kasar nan, abin kunya ne.
Ya ce ya kamata gwamnati ta sani rufe makarantun kasar nan ya sanya jahilci, ya dami al’ummar kasar nan. Don haka gwamnati ta sake bude makarantun kasar nan, kamar yadda ta bude sauran wurare, domin ‘ya’yan al’ummar Najeriya su koma su ci gaba da karatu.
Sheikh Jingir ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su rabu da kowa su koma ga Allah, domin ya warware masu matsalolin da suke  damunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here