Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Daukar Ma’aikata 774,000

1
483

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikta na musamman da majalisar dokoki ta dakatar.

Gwamnatin ta sanar da kaddamar da shirin ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shirin wanda ma’aikatar kwadago ke jagorantar, daga cikin matakan rage radadin annobar korona.

Za a dauki mutum 1,000 daga kowani karamar hukuma 774 da ke kasar, sannan kwamitocin jiha za su kula da shirin.

“ An kaddamar da kwamitocin zaben ma’aikatan na jiha kuka sun fara aiki,” cewar gwamnatin tarayya ta shafinta na Tuwita.

Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

A wani taro da suka yi a watan Yuni, mambobin kwamitin sun kusa bai wa hammata iska tsakaninsu da ministan inda daga bisani suka koreshi daga majalisar.

Amma Keyamo ya zargesu da yunkurin kwace daukar aikin tare da son amshe guraben don amfanin kansu da makusantansu.

Ya kara da zargar ‘yan majalisar da kokarin kalubalantar hukuncin shugaban kasar.

Ya ce ‘yan majalisar sun dauki mataki da ya fi karfinsu.

Majiyarmu ta gano cewa Keyamo ya samu ganawa da shugaban kasa inda ya bayyana mishi abinda ya faru a majalisar a kan shirin.

Shugaban kasar ya matukar fusata da yadda ‘yan majalisar ke son yin katsalandan a al’amarin da ya shafi masu zartarwa.

Ya bukaci ministan da ya ci gaba da shirin kuma ya tabbatar da an yi shi bisa tsarin da ya dace na shari’a.

Ya kara da bukatar darakta janar na NDE da ya tsayar da duk wani tsari na daban a kan shirin wanda yake yi tare da kwamitin majalisar tarayya.

An kuma tattaro cewa, ministan shari’a, Abubakar Malami, ya rubuta wasika ga ‘yan majalisar da su kiyaye iyakokinsu.

A baya majiyarmu ta ruwaito cewa za a bai wa gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar tarayya da ministoci gurbi na musamman a ayyuka 774,000 da gwamnatin tarayya za ta dauka.

Kwamitin zaben ma’aikatan ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin sanar da yadda daukar wadanda za su ci moriyar shirin za ta kama.

Shugaban kwamitin a jihar Bauchi, Sanusi Aliyu Kunde, ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin na jihar.

1 COMMENT

  1. Hakan daakayi yayi Amma da karace zaaturawa Kowane jiha sukawo nasu mutum 1000 inanyi haka to antashi daga wannan gefe ankoma wani gefe abunda ake gudu zaifaru taidda yaran marassa galihu bazasu Sami Daman shiga Cikin wadda zaadaukaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here