Raɗaɗin Ciwo Ya Sa Wani Mutum Ya Feɗe Cikinsa Da Wuƙa A Kaduna

0
752

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

SAKAMAKON raɗaɗin ciwo na gyambon ciki wato Ulcer da ya addabi wani magidanci, ya sanya mutumin ya feɗe cikinsa da wuƙa a Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan abun al’ajabi ya faru ne a garin Lere da ke Kudancin jihar ta Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, raɗaɗin ciwo na gyambon ciki ya sanya Hashimu Muhammad ya yi amfani da wata ‘yar karamar zabira wajen buɗe cikinsa ko zai ɗan samu sa’ida.

A yayin tattaunawa da wata ƙanwar Hashimu, ta bayar da shaidar cewa, ɗan uwan nata ya daɗe yana fama da cutar gyambon ciki, sai dai fa a wannan karo lamarin ya ƙara tsananta.

Majiyarmu, ta ce a halin yanzu Hashimu yana can yana fama da jinya a babban asibitin garin Lere cikin mawuyacin hali karkashin kulawar mahukunta lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here