Sojojin Najeriya Sun Saki Yaran Boko Haram 183

0
279

Rahoton Z A Sada

RUNDUNAR sojojin Najeriya ta ce ta saki yara 183 da aka kama bisa zargin alaka da kungiyar Boko Haram.

An saki yaran, da shekarunsu ke tsakanin shekara takwas zuwa 18, bayan an wanke su daga dangantaka da kungiyar.

Yaran, wadanda suka hada da mata takwas da maza 175, an sake su ne a ranar Litinin a garin Maiduguri na jihar Borno.

A halin yanzu an kai yaran cibiyar kula da yara ta gwamnati, inda ake yi musu rajista tare da magani.

Ofishin asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a Najeriya, ya ce zai yi aiki da jihar Borno domin tallafa wa yaran.

Bayan sun samu kulawa, za a hada yaran da iyalansu. A baya dai ana sukar gwamnatin kasar kan tsare yara.

A shekarar 2016, kungiyar kare hakikin bil’Adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa mutum 149, ciki har da yara 11 da kuma jarirai sun mutu a wani gidan wakafi da ke Maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here