Ajiye Bindiga 1 Mu Ba Ka Shanu 2 – Matawalle Ga ‘Yan Bindiga

0
253

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta shirya ba da shanu biyu da duk bindigar AK47 da kowane dan bindiga ya ajiye a jihar.

Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da ya karbi bakuncin manyan jagororin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari ya tura tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso yamma.

Jagororin su ne Sifeto Janar na hukumar ‘yan sanda , IG Mohammed Adamu, Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi, da sauran su.

A cewarsa, “Ga duk makamin da tubabben dan bindiga ya ajiye, za a maye masa da shanu biyu.” “Ba mu son ba  su kudi, saboda kada suyi amfani da shi wajen sayen sabbin makamai.” “Mun ce za mu saka musu da shanu, ‘yan Fulani ne kuma suna bukatar shanuu domin jin dadin arziki.”

“Hakazalika mun fada wa ‘yan bindiga su wargaza dukkan wata daba da suke da ita a cikin daji. Ba za mu lamunci ‘yan bindigan da aka amshi makamansu su koma cikin daji da zama ba.”

“Mun ce su zaba cikin dawowa cikin gari cikin jama’a ko a ba su dukiya su zauna inda suke domin fara sabuwar rayuwa.” “Yawancinsu suna zama ne cikin daji karkashin bishiyoyi da bukka. Shi ya sa muka kirkiro shirin RUGA domin taimaka musu.”

Gwamna Matawalle ya kara da cewa jihar Zamfara ce cibiyar ‘yan bindiga a Najeriya kuma idan jami’an tsaro za su iya dakile su a jihar, sauran sassan yankin arewa maso yamma za su huta.

Ya ce: “Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne dukkan shugabannin ‘yan bindigar na jihar Zamfara.” “Muna bukatar hukumomin tsaro su yi shiri na musamman.”

“Ya kamata a samu hadin kai tsakanin hukumomin tsaro saboda lokacin da aka kai musu hari a Katsina, jihar Zamfara, Sokoto da Kebbi suke guduwa.”

IGP Adamu a jawabinsa, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya umurcesu su kawo karshen lamarin tsaro a kasar saboda hakan na daminsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here