Anya Julius Berger Za Ta Iya Kammala Kwangilar Da Shugaba Buhari Ya Bata?- Kwamiti

0
275

Rahoton Z A Sada

KWAMITIN ayyuka na majalisar wakilan Najeriya ya bayyana fargabar cewa da wuya kamfanin Julius Berger da ke gudanar da wasu ayyuka da shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi kwangila ‘ya iya kammalawa nan da shekara uku.

Yanzu haka dai kwamitin ya gayyaci hukumar gudanarwar kamfanin domin jin halin da ake ciki game da aiyukan.

Shugaban kwamitin Hon. Kabiru Abubakar Bichi, ya shaida wa BBC cewa majalisarsu ta damu kan yadda ayyukan ke tafiyar hawainiya.

”Kusan shekara biyu kenan da fara aikin hanyar Abuja zuwa Kano, kuma alkawarin da suka yi wa gwamnati shi ne za su kammala cikin wata 36.

Mun duba cewa bai fi wata tara zuwa goma ne suka rage musu a yanzu haka ba, shi shugaban kasa ya damu yanzu haka don ganin an kammala wadannan ayyuka”.

Ayyukan sun hadar da samar da muhimman hanyoyi uku da gwamnatin ke tunkahon fara aiwatarwa, da suka hadar da hanyar Abuja zuwa Kano, da ta Legas zuwa Ibadan,

Sai kuma babbar gadar da ta hade yankin kudu maso gabashin kasar da sauran sassan Najeriya, wadda aka fi sani da Second Niger Bridge.

Ya ce kamfanin ya shaida musu cewa za su kammala aikin a kan lokacin da aka gindaya, amma masu sanya ido na majalisa na da shakku kan haka, saboda har yanzu, ba a cimma kashi daya cikin uku na aikin da ake yi ba.

Aikin titin Abuja zuwa Kano

Shi dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ware wa aikin kudade na musamman karkashin hukumar NSIA da ke bibiyar ayyukan gwamnatin kasar.

Sai dai kwamitin ayyuka na majalisar ya ce yanzu haka yana duba yiwuwar ba wa gwamnati shawarar raba ayyukan gida uku don bai wa karin wasu kamfanoni, maimakon kamfanin Julius Berger kadai.

Kwamitin dai ya kuma nemi jami’an kamfanin su sake bayyana nan da mako biyu, saboda bayanan da suka gabatar musu yayin zaman da suka yi ranar Alhamis ya gaza gamsar da ‘yan majalisar.

Yan Najeriya da dama na ci gaba da korafi a kan tafiyar hawainiya da ayyukan ke yi, abin da ke tilasta wa direbobi da matafiya shawo tsawon lokaci fiye da yadda aka saba a yayin tafiya.

Ana kuma samun karuwar hadurra a kan hanyoyin, abin da ‘yan majalisar suka ce ya zama dole a yi la’akari da shi don yin abin da ya dace.

Aikin gadar Second Niger Bridge

Majalisar wakilan Najeriya ta amince ta fara gudanar da bincike kan yadda ake gudanar da ayyukan ne yayin muhawarar da ta tafka kan batun a zamanta na ranar 27 ga watan Fabrairun 2019.

Wannan gayyata ta yanzu ita ce ta biyu tun fara aiwatar da binciken, kuma cikin wadanda aka gayyata har da jami’an ma’aikatar ayyuka ta Najeriya.

Ta kuma gayyaci shugabancin hukumar kare aukuwar hadurra ta kasar domin jin ba’asi game da karuwar hadurran da ake samu a kan wadannan hanyoyi.

Yan majalisar na zargin kamfanin dake gudanar da aikin da yin wasarere, duk da kudin da ya karba, kana ya shaida musu cewa baya fama da wata matsalar kudi da za ta hana shi gudanar da aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here