Mutum 6 Za Su Maimaita Hidimar Bautar Kasa A Kano – NYSC

0
209

Daga Usman Nasidi.

A RANAR da wasu ke farin ciki na kammala bautar kasa ta NYSC, wasu ko murnarsu ta koma ciki a sakamakon wajabta musu maimaita shekara daya ta bautar da za su yi a jihar Kano.

Shugabar hukumar NYSC ta jihar Kano, Hajiya Aisha Mohammad ta bada wannan sanarwa a yayin bikin yaye rukuni na biyu na masu hidimar kasar da suka kammala a bana.

Aisha ta bayyana cewa, mutanen shida ne za su maimaita shekara guda ta bautar kasa, yayin da kuma hukumar ta tsawaita hidimar wasu mutum 16 sakamakon laifuka iri-iri da suka aikata.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi bikin gabatar da takardun shaidar kammala bautar kasar wanda aka gudanar a sakateriyar hukumar da ke kan titin Gwarzo a kanon Dabo.ano State.

Ta bayyana cewa, matasa 2,677 ne suka kammala bautar kasarsu salin alin a jihar Kano ba tare da samun wata tangarda ba.

Shugaban hukumar ta ce duk cikin masu bautar kasar babu wanda cutar korona ta harba har suka kammala hidimarsu ta tsawon shekara guda a jihar.

Ta kara da cewa tuni hukumar ta yi tanadin duk wasu shirye-shiryen da suka wajaba don tabbatar da komawar masu bautar kasar zuwa jihohinsu na asali cikin aminci.

Ta gargade su a akan su tabbatar sun kasance sanye cikin kakin da hukumar ta basu na hidima yayin da zasu koma gidajen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here