Bashin CBN Maras Ruwa Zai Haɓaka Arziƙin Musulmi – Majalisar Musulunci

1
834
Mai alafarma Sarkin Musulmin Najeriya

Rahoton Z A Sada

MAJALISAR ƙoli kan harkokin addinin musulunci a Najeriya ta buƙaci al’ummar musulmi su zabura wajen neman rancen kuɗi maras ruwa da babban bankin ƙasar ya ɓullo da shi ga masu ƙananan sana’o’i.

Majalisar wadda Sarkin Musulmi mai alfarma Alhaji Sa’ad Abubakar III ke jagoranta ta ce a baya musulmai ba sa cin gajiyar bashi daga gwamnati saboda ruwa, lamarin da haddasa ƙaruwar talauci a tsakanin al’umma.

@CENBANK

Majalisar ta ce ta yi matuƙar farin ciki kan wannan dama kuma ta yaba wa babban bankin ƙasar da gwamnatin Najeriya har ma da ‘yan majalisa waɗanda ta ce sun yi tsayuwar daka wajen ganin tabbatar wannan fata.

Mataimakin babban sakatare na majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya ce musulmin Najeriya sun zama koma-baya kar harkokin bunƙasa tattalin arziƙi saboda rashin samun rance maras ruwa.

“Duk wani abu da za a kawo na tallafi da bunƙasa tattalin arziƙi (a baya) sai ka ga mutanenmu ba za su iya mu’amala da wannan ba. Sai ka ga mutum ya gwammace ya zauna da talaucinsa,” in ji shi.

Ya ce amma yanzu musulmi kai tsaye suna iya neman irin wannan rance ba tare da wata fargaba ko tunani ba, don bunƙasa sana’o’i.

Farfesa Salisu Shehu ya ce matakin wata babbar dama ce da za ta taimaka wajen haɓaka tattalin arziƙin ba kawai al’ummar musulmi ba, har ma ga ɗaukacin ƙasar gaba ɗaya.

A ranar 14 ga watan Yulin 2020 ne babban bankin ya sanar da ɓullo da shirin samar da rance maras ruwa ga fannoni daban-daban na masu sana’o’i da kuma matsakaitan ‘yan kasuwa.

Mataimakin babban sakataren ya yi kira ga masu ƙananan sana’o’i da masu harkokin noma da masu harkokin ilmi da cibiyoyi da makarantun lafiya su tashi don cin gajiyar wannan shiri.

Ɗaya daga cikin shirye-shiryen da babban bankin Najeriyar ya bullo da shi har da shirin zaburas da bunƙasar harkokin noma wato Accelarated agricultural development scheme ga matasa.

A cewar wata sanarwa da babban bankin ya wallafa a shafinsa na tiwita, manufar shirin ita ce shigar da matasa aƙalla 370,000 cikin harkokin noma a faɗin Najeriya cikin shekara uku mai zuwa.

Ya ce matakin, wani yunƙuri ne na rage rashin aikin yi tsakanin matasan ƙasar ‘yan kimanin shekara 18 zuwa 35 da kuma bunƙasa wadata ƙsa da abinci da ƙirƙirar ayyuka gami da baza komar tattalin arziƙi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here