Al’umar Dungurawa Sun Yaba Wa Dan Majalisa Saleh Marke.

0
450
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
SAKAMAKON aikin kammala masallacin Juma’a da dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Saleh Ahmed Marke ya yi a garin Dungurawa,  al’umar wannan yanki sun bayyana godiyarsu bisa wannan aiki na alheri da dan majalisar yayi kuma a daidai lokacin da ake bukatar sa.
Shi dai wannan masallaci mutanen gari ne suka fara tunanin samar da shi ta hanyar taimakon kai-da-kai, inda kuma  mutanen garin na Dungurawa da kewaye suka yi kokarin taimaka wa wannan yunkuri na gina masallacin Juma’a babba domin ci gaba da gudanar da ibada cikin yanayi mai kyau.
Bayan aikin gini ya yi nisa sai dan majalisa Saleh Marke ya ci gaba da aikin ginin har zuwa karshen sa wanda kuma cikin yardar Ubangiji ranar Asabar din da ta gabata aka damka  masallacin ga kwamitin  kula da shi domin ci gaba da ibada kamar yadda aka yi ta kokarin samu.
Liman Alhaji Malam Hassan Dungurawa, wanda shi ne limamin da ya shafe fiye da shekaru 50  yana jagorancin sallah a wannan gari na Dungurawa ya ce ko shakka babu, samun wannan masallaci na Juma’a ya yi matukar yi masu dadi duba da yadda garin yake kara bunkasa ta kowane fanni, tare da yin addu’oi na fatan alheri ga dukkanin wadanda suke da hannu wajen ganin an sami babban masallacin Juma’a a wannan gari na Dungurawa.
Haka kuma dukkanin mutanen da suka zanta da wakilinmu sun yi matukar godiya ga dan majalisa Saleh Ahmed Marke saboda kokarin da ya yi har Allah ya sa aka kammala ginin wannan masallaci na Juma’a a wannan gari na Dungurawa kuma a zamanin wakilcinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here