Home Kasuwanci Yaran Da Bam Ya Tashi Da Su A ‘Yanmama Sun Kai 7

Yaran Da Bam Ya Tashi Da Su A ‘Yanmama Sun Kai 7

0
343
Gwamna Masari na jihar Katsina

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN jihar Katsina ta ce ta samu rahoton mutuwar yarinya ta bakwai cikin yaran da wani abu da ake zargin bam ne ya tashi da su cikin wata gona a ƙauyen ‘Yanmama na ƙaramar hukumar Malumfashi.

Wani mataimaki na musamman ga gwamnan jihar, Muhammadu Garba ya faɗa cewa, tashin farko yara shida ne suka rasu, sai wadda suka samu rahoton mutuwarta daga bisani.

“Za a kawo ta yanzu a haɗa su, su bakwai ke nan a yi musu jana’iza. Akwai kusan aƙalla guda biyar da ke asibiti ana kula da su,” inji shi.

Wannan ne dai karon farko da aka samu irin wannan al’amari na tashin abin fashewa a jihar, mai fama da tarzomar ‘yan fashin daji, abin da kuma ya tsananta fargabar da ake da ita kan ƙaruwar lamarin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tuni aka tura ƙwararru kan harkar abubuwa masu fashewa don gudanar da bincike game da wannan al’amari.

Shi dai Muhammadu Garba ya ce yaran da abin ya faru da su, sun je gonar ne don yin ciyawa. “Sai suka tsinci wani abu mai nauyi, sun ɗauke shi da zimmar za su buɗe shi, su ga ko mene ne”. Ya ce wasu daga cikin yaran sun ja hankalin sauran abokansu cewa abin da suka tsinta “bam ne”. Yayin da sauran suka ce ba bam ba ne.

Hukumomi dai ba su bayyana taƙamaimai ko mene ne abin da ya fashen ba. Hakazalika, babu masaniya game da yadda aka yi abin fashewar ya je wannan gona. Yayin da wasu mutane ke ci gaba da tambayoyi kan ko an ɗana abin fashewar ne da gangan, ko kuma wani ne ya jefar da shi a cikin gonar wadda take gefen titi.

A cewar Muhammadu Garba matar da ke cikin gonar tare da yaran da suka tsinci abin fashewar ta tabbatar wa jami’an tsaro cewa ba shakka abin da suka gani ya fi kama da gurnetin da aka nuna mata.

Ya ce: “jami’an tsaro sun kawo nau’o’in abubuwan fashewa inda suka nuna mata ko za ta iya shaida mai kama da abin da ta gani a hannun yaran”.

Matar wadda Allah Ya kuɓutar tare da ‘ya’yanta ta umarci ‘yarta ne ta mayar wa yaran da suka fara tsintuwar, bayan da suka dawo suka ce su fa suna son kayansu, inji shi.

Uwar yaran da suka kuɓuta, wadda ba a bayyana sunanta ba, ta ce ita da kanta ta bayyana tababa lokacin da wani daga cikin yaran da suke tare ya ce ba shakka abin da suka tsinta “bam ne”.

“Cikin gonar Alhaji Usaini, sai ɗan babban cikinsu ya ce bam ne. Ni kuma sai na ce kai! Wanne irin bam, a cikin gona” inji ta.

Ta ce har sun mayar sun ajiye, su ma waɗancan yaran sun kama hanya sun tafi, sai ƙaramin ɗanta ya nemi izini ta bar shi ya ɗauka don kuwa kayan gwangwan ne.

“Sai na ce da ‘Allah can,  wannan ba bam ba ne. Ƙila cikin motocin nan da ke wucewa ne wani abu ya fita. Ƙila waya ce ciki. Sai ya ce to zai ɗauka ya kai wa mai gwangwan”.

Waɗancan yaran na jin haka sai suka dawo suka ce su ne suka tsinta a ba su abinsu, inji matar.

A cewarta sun kama hanya (ita da ‘ya’yanta) sun yi nisa, sai suka ji ƙarar abin da ya fashe. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ASP Gambo Isa ya ce yaro biyar a take suka rasu bayan fashewar. Ya ce jami’ansu na can cikin gonar don ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: