A Kan Maryam Yahaya, Wani Matashi Ya Sha Fiya-Fiya

1
716
Daga Usman Nasidi.
WANI matashi da ya yi tattaki tun daga jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, don ganin jaruma Maryam Yahaya, ya so ya yi ajalin kansa saboda rashin cikar burinsa na ganin jarumar tashi.
Kamar yadda jama’ar da ke wurin suke bayyanawa, matashin ya kwana a Unguwar Zoo Road, inda ya zama kamar dandalin taruwar jaruman Kannywood don ya ga jaruma Maryam Yahaya amma bai samu ganin ta ba.
Hakazalika, an ji wasu na cewa sau uku matashin ya yi yunkurin shan fiya-fiya, kafin daga bisani ya bulbulawa cikinsa maganin kashe kwari da ya kusa zama ajalinsa.
An dai samu ceto rayuwar matashin ta hanyar ba shi agajin madara.
Sai dai duk da wannan abu da ke faruwa, Jaruma Maryam Yahaya ba ta san yana yi ba ko kuma ta yiwu ba ta samu ko da labari ba.
Ko da kuwa ta samu labari, ba ta yi yunkurin yin wani abu a kai ba domin ko a shafinta na sada zumunta ba ta nuna alhini ko jaje ga wannan dan kasadar ba da ya so salwantar da rayuwarshi saboda ganin ta ba.
Matashin dan asalin karamar hukumar Gashua ta jihar Yobe, ya je jihar Kano ne saboda kaunar jaruma Maryam Yahaya da yake yi.
Bayan duk kokarin ganinta da ya yi amma hakan ya gagara, ya yanke shawarar buga waka, ta yiwu ta hakan zai samu su hadu cikin sauki.
Sai dai hakan ya tashi a tutar babu. Daga nan ne ya sha fiya-fiya a cikin fura inda ya fadi rai a hannun Allah.
Babu jimawa hukumar Hisbah ta aiko da mota inda aka kwashe shi zuwa asibiti don ceto rayuwarsa.
A zantawar manema Labarai da saurayin Kamal bayan farfadowarsa a asibiti, ya ce a halin yanzu ya hakura amma fa son Maryam Yahaya na nan a ransa daram.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here