Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar NSCDC

0
263
Daga Usman Nasidi.
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa’adin Kwamandan Rundunar Tsaron Al’umma ta Najeriya (NSCDC), Abdullahi Gana Muhammadu.
Shugaban kasar ya amince a tsawaita wa’adin shugaban hukumar NSCDC daga yanzu har zuwa tsawon watanni shida.
Mai magana da yawun Kwamanda Janar Gana, Ekunola Gbenga, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai.
Sabanin rade-radin da ke yaduwa na cewa Buhari ya sabunta nadin mukamin shugaban na NSCDC na tsawon shekaru biyar da zai kare a ranar 17 ga watan Yulin 2020, Mista Gbenga ya ce kanzon kurege ne.
Mista Gbenga ya ce wannan zantuttuka ne kawai na shaci fadi da wasu ke kirkira domin su haifar da matsala a hukumar NSCDC.
“Ya kirayi al’umma da su yi watsi da wannan jita-jita da babu abinda za ta tsinana face ta kai su kuma ta baro”.
Ya ce Buhari ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar NSCDC ne ta hannun Ministan harkokin cikin gida , Rauf Aregbesola, kuma za ta fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Yulin 2020.
An tsawaita wa’adin Kwamandan na NSCDC bisa la’akari da kwazon aiki da kuma rawar da ya taka wajen bunkasa harkokin gudanarwa da kuma inganci a hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here