NAF Ta Bayyana Wanda Ya Kashe Arotile, Ta Mika Lamarin Ga ‘Yan Sanda

0
280
Daga Usman Nasidi Da Z A Sada
RUNDUNAR sojin saman Najeriya a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, ta bayyana direban motar da ya bige marigayiya Tolulope Arotile, matukiyar jirgin yakinta.
Daraktan yada labarai na rundunar, Ibikunke Daramola, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro a Abuja.
Daramola ya ba da sunan tsohon dan ajin su Arotile da ya kasheta a matsayin Nehemiah Adejoh.
Kakakin NAF ya kara da cewa za a mika al’amarin ga ‘yan sandan Najeriya saboda batun ya shafi farar hula.
Ya ce an mika wannan bayanin ga ‘yan uwan matukiyar jirgin wadanda ke ci gaba da zaman makokinta.
A yayin ba da rahoton binciken farko da NAF ta yi, kakakin ya ce marigayiya Arotile ta hadu da tsofaffin ‘yan ajinsu a makarantar sakandire a ranar da abin ya faru.
Ya ce, “Nehemiah Adejoh, Igbekele Folorunsho da Festus Gbayegun sun wuce ta a wata mota kirar Kia Sorrento SUV da lambar rijista AZ 478 MKA.
“Dukkan su ukun farar hula ne kuma suna rayuwa ne a wajen barikin cikin Kaduna amma suna kan hanyarsu ta zuwa wurin wata Chioma Ugwu, matar Squadron Leader Chukwuemeka Ugwu wacce ke zama a kwatas din Ekagbo.
“Bayan gane ‘yar ajinsu Arotile, Adejoh da ke tuki ya koma baya da motar don samunta. Motar ta bigeta inda kanta ya bugu a kasa. Motar ta hau wani sashi na jikinta wanda hakan ya sa ta samu raunuka.”
Daramola ya ce an gaggauta mika Arotile asibiti amma wurin karfe 4:45 na yamma aka tabbatar da mutuwarta.
Ya yi bayanin cewa a take aka kama ‘yan ajin nasu inda aka yi musu gwajin giya amma babu wani nau’i maye ko warin barasa a tattare da su.
“Sai dai an gano cewa direban motar, Mista Nehemiah Adejoh, bai da lasisin tuki mai aiki.
“Kasancewar lamarin da ya shafi farar hula ne, za a mika shi ga rundunar ‘yan sandan Najeriya domin ci gaba da bincike da kuma mika wadanda ake zargin a kotu kamar yadda doka ta tanadar,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here