‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojojin Najeriya Kwanton Bauna, Sun Kashe 16 A Katsina

0
320
Daga Usman Nasidi.
A wani hari na samame da ‘yan daban daji suka kai jihar Katsina a ranar Asabar, ya salwantar da rayukan dakarun soji 16, yayin da 28 suka jikkata.
Da misalin karfe 6.13 na Yammacin ranar Asabar yayin da dakaru suka fita sintiri a yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, ‘yan bindiga sun yi musu kwanton bauna, inda suka rika yi musu ruwan wuta daga wani saman tsauni.
Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Manjo, Kyaftin, da Laftanar kamar yadda wata majiya daga dakarun sojin ta shaida wa manema labarai.
An tattaro cewa wasu ‘yan ta’adda biyu sun raunata yayin da dakarun sojin suka yi yunkurin mayar da martani.
Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya samu labarin harin.
Jihar Katsina wadda ta kasance mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, a baya bayan lamari na rashin tsaro ya ci gaba da tabarbarewa da har ya kai mataki na intaha.
A jihar Katsina kadai, an ruwaito cewa ta’addanci ya salwantar da rayukan fiye mutane 2000, da tarwatsa alkaryu 5000 yayin da kuma aka watsa mutane fiye da 33,000 daga matsugunnasu.
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da samun labarin mutuwar cikon mutum na bakwai cikin yaran da bam ya tashi dasu a cikin wata gona a kauyen ‘Yanmama da ke karamar hukumar Malumfashi.
Hadimi na musamman ga Gwamna Aminu Masari, Muhammadu Garba ya bayyana cewa a tashin farko yara shida ne suka rasa rayukansu, sai kuma wacce a yanzu suka samu labarin mutuwarta.
Ya ce: “Za a dauko ta yanzu a hada da sauran mutum shidan domin yi musu jana’iza. Akwai kusan akalla guda biyar da ke asibiti ana kula da su.”
Wannan shine karo na farko da aka samu irin haka a jihar , wacce ke mai fama da hare-haren ‘yan fashin daji, inda hakan ya kara tsananta fargaba a zukatan al’umma.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tuni aka tura masana a kan harkar abubuwa masu fashewa domin su gudanar da bincike game da wannan lamari.
Har ila yau hadimin gwamnan ya bayyana cewa yaran da abin ya faru da su, sun je gonar ne domin yin ciyawa.
“Sai suka tsinci wani abu mai nauyi, sun dauke shi da niyar za su bude shi, su ga ko mene ne”, in ji shi.
Ya ce wasu daga cikin yaran sun ja hankalin sauran abokansu cewa abin da suka tsinta “bam ne”.
Yayin da sauran suka ce ba bam ba ne. Zuwa yanzu dai hukumomi basu sanar da ainahin ko menene abun da ya fashen ba, sannan kuma babu tabbaci kan yadda abun ya isa wannan gona.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here