Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Mana A Katsina, Dakaru 3 Ne Kawai Suka Mutu – Rundunar Soji

0
249
Sojoji ba sa sanya baki a batu irin na 'yan siyasa a Najeriya?

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR sojin Najeriya ta yi karin haske dangane da asarar da ta yi a hannun ‘yan daban daji yayin da suka kai wa dakarunta hari a karamar hukumar jibiya ta jihar Katsina.

Kafofin labarai da dama sun ruwaito cewa, harin da ‘yan bindiga suka kai wa wata rundunar sojin kasa a jihar Katsina, ya salwantar da rayukan dakaru 16.

Sai dai da take mayar da martani da fayyace ainihin asarar da harin ya janyo mata, rundunar sojin ta ce dakarunta 3 ne kacal suka riga mu gidan gaskiya.

Cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar a ranar Lahadi, ta ce dakarun Operation Sahel Sanity, sun kashe akalla ‘yan daban daji 17 yayin wata arangama a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Hukumar tsaron ta kuma ce dakarunta sun samu nasarar kwato muggan makamai da suka hadar da bindigu kirar AK 47, alburusai da kuma babura bakwai bayan sun fafata da ‘yan ta’adda.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar Operation Sahel Sanity, Bernard Onyeuko ya sanar, an yi asarar rayukan dakaru uku yayin da kuma wasu dakarun hudu suka jikkata a filin daga.

Sai dai wannan ikirari da rundunar sojin ta yi ya saba wa rahoton da wani babban jami’in soji ya gabatar wa manema labarai.

Majiyar mai tabbas ta sanar da cewa, akalla rayukan sojoji 16 ne suka salwanta ciki har da wasu manyan dakaru 3 yayin da wasu 28 suka jikkata a harin na kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai a ranar Asabar.

Majiyarmu ta samu labarin cewa, a wani simame da ‘yan daban daji suka kai jihar Katsina a ranar Asabar, sun salwantar da rayukan dakarun soji 16, yayin da 28 suka jikkata.

Da misalin karfe 6.13 na Yammacin ranar Asabar yayin da dakaru suka fita sintiri a yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, ‘yan bindiga sun yi musu kwanton bauna, inda suka rika yi musu ruwan wuta daga wani saman tsauni.

Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Manjo, Kyaftin, da Laftanar kamar yadda wata majiya daga dakarun sojin ta shaidawa manema labarai.

An tattaro cewa wasu ‘yan ta’adda biyu sun raunata yayin da dakarun sojin suka yi yunkurin mayar da martani.

Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya samu labarin harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here