Sabon Harin ‘Yan Bindiga: An Kashe Mutane 19 A Kaduna

0
457

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AKALLA mutane 19 rahotanni suka bayyana cewa sun rasa ransu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Kukum Daji a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Lahadi.

Kazalika, jaridar ta bayyana cewa wasu mutane 30 sun tsallake rijiya da baya bayan sun tsira da munanan raunuka.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun dira kauyen tare da yi wa mutane kisan gilla.

Mista Yashen Titus, shugaban kungiyar cigaban kauyen Kukun Daji, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa ‘yan bindigar sun bude wuta a wurin wani taron biki da ake yi a wani gida a kauyen.

Ya kara da cewa ‘yan bindiga sun dira kauyen da misalin karfe 10:35 na dare tare da fara yin harbin ‘kan mai uwa da wabi’.

“Suna dauke da muggan makamai, mutane 17 daga cikin mutanen suka kashe sun mutu nan take a wurin da suka harbe su.

“An garzaya da mutane 32 zuwa asibiti domin ceton rayuwarsu, amma, abin takaici, biyu daga cikinsu sun mutu a asibiti.

“A yanzu haka da nake magana da ku, bamu san inda mazauna kauyen da dama suka shiga ba tun bayan da suka gudu daga gidajensu a lokacin da ‘yan bindigar suka kawo hari.

“Mu na jin tsoron shiga jeji domin fara nemansu, saboda har yanzu ba a kawo jami’an tsaro yankin ba,” a cewar Titus.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da kai harin.

Sai dai, ya bayyana cewa har yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta gama tattara alkaluman adadin mutanen da suka mutu ba.

“Tabbas an kai hari kauyen Kukum Daji da ke yankin karamar hukumar Kaura a daren jiya (Lahadi).

“Mun tura jami’an tsaro zuwa yankin, amma ya zuwa yanzu ba zamu iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa ransu ba. Zan tuntubeku da zarar mun samu karin bayani ,” a cewar Jalige yayin magana da manema labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here