Wani Dan Damfara Ya Yi Kokarin Halaka Kansa A Hannun ‘Yan Sintiri

0
254

Isah Ahmed Daga Jos

WANI da ake zargi da aikata laifin damfarar wasu mutane uku kudade har N980,000 mai suna Aliyu Ibrahim, ya yi kokarin hallaka kansa a hanun jami’an  rundunar ‘yan kungiyar  sintiri ta Vigilante ta Jihar Kaduna, reshen Karamar Hukumar Lere.

Wannan al’amarin dai  ya faru ne a ranar Juma’ar nan da ta gabata, a ofishin rundunar da ke garin Saminaka.

Da yake zantawa da wakilinmu kan yadda  al’amarin  ya faru, Kwamadan rundunar kungiyar ta Viglante   reshen Karamar Hukumar Lere, Yahaya Isma’il  ya bayyana cewa  wannan abin al’ajabi.  Ya faru ne bayan da suka kama wannan mutum, suna tuhumarsa da laifin yi wa wasu mutane uku damfarar kudi N980,000 da niyar zai sayar masu da kayan gini, a Abuja.

Ya ce sun kama wannan mutum ne a garin Saminaka, bayan da suka yi amfani da wani jami’insu, wanda ya kira shi a waya cewa ya zo zai sayar masa, da wasu kaya.

‘’Ganin ya shiga hannu, shi ne ya yi kokarin kashe kansa, ta hanyar cire igiyar wandonsa ya daure marainarsa don ya kashe kansa, saboda  kunyar wannan damfara, da ya aikata. Duk da bamu yi masa komai ba a wannan ofishi. Lokacin  da muka fahimci wannan kokari da yake yi na hallaka kansa, nan take muka zo muka kubutar da shi.

Kwamadan ya yi bayanin cewa za su mika wannan mutum ga jami’an ‘yan sanda, domin a ci gaba da bincike don gurfanar da shi, a gaban kotu.

Ya yi  kira ga sauran jami’an tsaro su rika lura da mutanen da suke tsarewa, don  gudun kada su kashe kansu a lokacin da suke tsare a wajen su, domin za a iya cewa sune suka kashe su.

Da yake zantawa da wakilinmu wanda ake zargi da aikata damfarar  Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa, gaskiya ne ya karbi wadannan kudade da manufar zai sayar wa wadannan mutane  da kaya ne, amma ya je kashe su wajen neman takardar lasisin shigo da shinkafa daga waje,  a wajen wasu jami’an kwastan, kuma har ya zuwa wannan lokaci bai sami lasisin ba.

 Ya ce gaskiya ya yi nadamar wannan abu da ya faru, don haka yana  tuba ga hukuma da wadannan mutane da na yiwa wannan abu.

‘’ Dalilin da ya sa na yi kokarin kashe kaina shi ne ban taba tsintar kaina, a wannan yanayi ba. Don haka shaidan ya raya mani, gara mutuwa ta da in ci gaba da rayuwa’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here