Home Kasuwanci Buhari Ya Roƙa Wa Sarki Salman Na Saudiyya Sauƙin Ciwon Mafitsara

Buhari Ya Roƙa Wa Sarki Salman Na Saudiyya Sauƙin Ciwon Mafitsara

0
846

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wa Sarki Salman na Saudiyya fatan samun lafiya wanda yanzu yake kwance a gadon asibiti.

A ranar Litinin ne aka kwantar da Sarki Salman asibiti inda rahotanni suka ce yana fama ne da matsalar mafitsara.

Shugaba Buhari da Sarki Salman na Saudiyya

A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya yi masa addu’ar fatar samun sauki cikin gaggawa a madadinsa da kuma al’ummar Najeriya.

Ya kuma bayyana Sarki Salman a matsayin shugaba mafi nagarta da ya taɓa haɗuwa da shi a yayin mu’amularsa da sauran shugabannin duniya.

“Sarki Salman aminin Najeriya ne na haƙiƙa wanda bai taɓa kasawa ba ko nuna damuwa ta ko wane ɓangare kan dukkanin muhimman buƙatu da kyakkyawar alaƙa,” inji Buhari.

Bayanai dai sun ce masarautar Saudiyya ta tabbatar da cewa mafistararsa ce ta kumbura kuma ana ci gaba da bincike.

Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya – kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012. Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin Gwamnan Riyadh.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: