Home Kasuwanci Katsina: ‘Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 17 A Garin Zakka

Katsina: ‘Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 17 A Garin Zakka

0
881

Rahoton Z A Sada

AL’UMMAR garin Zakka a jihar Katsina sun ce wasu ‘yan bindiga da ba su san ko su waye ba sun kai masu hari inda suka sace mata 17 da kuma kwashe shanu da dukiyoyinsu.

Wani mazauni garin na Zakka da ke cikin ƙaramar hukumar Safana ya shaida wa manema labaru cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin ne tsakar daren Lahadi inda suka shafe sama da sa’a biyu suna fashi.

Gwamna Masari

Ya ce ‘yan bindigar sun shigo garin ne misalin karfe 12 na dare kuma suka fara harbin bindiga wanda ya razana mutanen garin wasu suka ruga daji wasu kuma suka boye a cikin karan dawa da gero.

“Sun kwashe shanu da dama da tumaki sannan suka shiga gida gida suna kwatar dukiyar mutane kafin su tafi da mata da ‘yan mata 17,” inji shi.

Amma ya ce ɓarayin sun mayar da wata yarinya ‘yar wata biyar da haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka ɗauka da ya ce su ma Allah ya kuɓutar da su. ‘Yan bindigar dai ba su kashe kowa ba a garin na Zakka wanda a bara aka taba kai wa hari. Ya zuwa tattara wannan rahoto, babu dai wani bayani da ya fito daga jami’an tsaro game da harin.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma sakamakon matsi da suke fuskanta daga ‘yan bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: