An Hana Yin Hawan Sallah A Masarautun Jihar Kano Biyar

0
339
Mustapha Imrana Abdullahi
MAJALISAR zartaswar Jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana hanin yin hawan Sallah a duk fadin Jihar.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya shaidawa manema labarai a lokacin wani taron manema labarai da ya yi a Kano.
Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa hakika bayan duba a tsanake da Gwamnatin ta yi ta hana yin hawan Sallah a dukkan masarautu biyar da ake da su a Jihar Kano baki daya.
“Dukkan sarakuna za su yi Sallah ne a masarautunsu tare da bin ka’idar hana yaduwar cutar Korona kamar yadda suke a tsare”.
Saboda haka ake yin kira ga daukacin jama’a da su kiyaye dukkan ka’idojin da aka shimfida a tsarin hana yaduwar cutar Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here