Ba Za A Buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa Da Ranar Sallah Ba

0
767
Rabo Haladu Daga Kaduna
MANJO Janar Mohammed Bin Wasl Al-Ahmadi, mataimakin shugaban jami’an tsaro na Masallacin Harami yayin aikin Hajji, ya faɗa ranar Talata cewa masallacin zai ci gaba da kasancewa a rufe a ranakun Arafa da Idin Babbar Sallah saboda hana bazuwar cutar korona.
Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruewaito shi yana cewa: Dakatar da sallah a cikin masallacin da harabarsa zai ci gaba da aiki. Mun shawarci mutanen garin Makkah da su karya azuminsu na Ranar Arfa a gaidajensu,” in ji shi.Manjo Janar Al-Ahmadi ya yi wadannan jawabai ne a yayin wani taron manema labarai inda ya sanar da kammala matakin farko na tsara Aikin Hajjin bana.
Ya ce tsarin tsaro na hajjin bana zai mayar da hankali ne kan tsaro da jin kai da batun lafiya.Mun mayar da hankali ne bana kan batun lafiya saboda yanayin da aka samu kai a ciki. Sauran matakan za a kammala su a kwanaki masu zuwa,” in ji Manji Janar Al-Ahmadi.Ya ce an sanya sabon tsari don lura da shiga da fitar mahajjata cikin Masallacin Haramin don tabbatar da cewa an bi dokar yin nesa-nesa da juna.Daga cikin matakan kariyar da aka dauka, an kebe hanyar zuwa wajen dawafi da na Safa da Marwa, sannan za a bar masu izini a hukumance su shiga harabar masallain in ji Manjo Janar Al-Ahmadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here