Home Kasuwanci Badaƙalar NDDC: Ko Akpabio Zai Bayyana Sunayen ‘Yan Majalisar Da Ya Ba...

Badaƙalar NDDC: Ko Akpabio Zai Bayyana Sunayen ‘Yan Majalisar Da Ya Ba Kwangila?

0
799

Rahoton Z A Sada

A YAYIN da wa’adin da majalisar dokokin Najeriya ta bai wa ministan ma’aikatar raya yankin Neja Delta kan fallasa ‘yan majalisar da yake zargi da cin gajiyar kaso mai tsoka na kwangilolin da hukumar NDDC ke bayarwa ke cika ranar Alhamis, ko me zai biyo baya?

Kakakin majalisar wakilan ƙasar Femi Gbajabiamila ne ya bai wa Godswill Akpabio umarnin bayan da ministan ya yi zargin cewa kashi 60 na kwangilolin hukumar an bai wa ‘yan majalisa ne ciki har da shugabanni biyu da suke jagorantar binciken baɗaƙala a hukumar.

Akpabio

Majalisar dai na gudanar da binciken almubazzaranci na fiye da naira biliyan 81, sama da dala 210,000 a hukumar.

An kafa hukumar ta raya yankin Neja Delta shekara 20 baya domin inganta rayuwar al’ummar yankin da ke da arzikin mai.

A ranar Litinin ne kuma bayan Shugaban hukumar ta NDDC, Daniel Pondei ya sha tambayoyi daga kwamitin majalisar aka ga ya kife kai kamar ya suma.

Daga nan aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa.

Ministan ma’aikatar raya Neja Delta yayin da ya bayyana gaban kwamitin a ranar Litinin, ya yi ikirari cewa “‘yan majalisar sune suka fi cin gajiyar kwangilolin da hukumar ta bayar.

Da aka tambaye shi ta yaya, ministan sai ya ce, “Yanzu na gama faɗin cewa muna da takardu da ke nuna cewa ‘yan majalisar dokoki ake ba wa akasarin kwangilolin na hukumar NDDC”.

Sai dai wannan iƙirarin ya fusata Kakakin majalisar wakilan, Mista Gbajabiamila inda ya ba da wa’adin sa’oi 48 ga ministan ya fitar da sunayen mutanen da suka ci gajiyar da kuma cikakken bayani kan kwangilolin da aka bai wa ‘yan majalisar ko kuma su fuskanci fushin doka domin dai ganin ya amsa umarnin majalisar.

‘Yan Najeriya na dakon ƙarin bankaɗa daga binciken da ake gudanarwa idan har aka wallafa ‘yan majalisar a jadawalin sunayen.

Godswill Akpabio dai tsohon ɗan majalisa ne kafin karɓar mukamin minista a Agustan 2019.

A baya-bayan nan ne kuma, tsohuwar shugabar hukumar NDDC Joy Nunieh ta zargi Akpabio da almundahana; ta shugabanci hukumar ne tsawon wata huɗu kacal kafin a kore ta.

Ms Nunieh ta zargi Akpabio da hannu a tsige ta inda ta ce ya sha matsa mata lamba ta yi rantsuwa don binne almundahanar da aka tafka a hukumar.

Ministan ya musanta zarge-zargen inda ya ce an sauke ta ne saboda “rashin girmama na gaba a aiki”.

A lokacin da mukaddashin shugaban hukumar ta NDDC, Mista Pondei da sauran jami’ai suka bayyana gaban majalisa, ya zargi shugaban kwamitin da ke bincikar hukumar ta NDDC, Olubunmi Tunji Ojo da cin hanci tare da ƙin amsa tambayoyin da kwamitin ya riƙa jefa masa.

A lokuta da dama, ana zargin ‘yan majalisa a Najeriya da aikata cin hanci ta hanyar karɓar kwangila daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da kuma yin cushe a kasafin kuɗi.

Daniel Pondei

Wani masanin shari’a ɗan Najeriya da ke zama a Burtaniya Barista Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa ko da ministan ya gaza fitar da sunayen, majalisar dokokin abu ɗaya kawai za ta iya yi shi ne “ba wa Shugaba Buhari shawarar sauke ministan daga kan muƙaminsa”.

“Shawara ce ba dole ba ne”. “A baya, mun ga yadda majalisar dokokin Najeriya ta ba da shawarwari ga shugaban amma ba ɗaya daga ciki daya aiwatar”.

“Misali buƙatar ‘yan majalisar ta sauya shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa arzikin ƙasar ta’annati Ibrahim Magu bata samu shiga ba a wajen shugaban”.

A cewar Barista Bulama Bukarti, idan zarge-zargen da aka yi wa ‘yan majalisar ya zama gaske, “‘yan majalisar da suka karɓi kwangiloli daga hukumar sun yi abin da ya saɓwa dokokin Najeriya”.

“SIdan aka saɓa dokokin majalisa kuma majalisar na iya yanke shawarar dakatar da ‘yan majalisar da aka samu da hannu tare da umartarsu sumayar da kuɗaɗen da suka karɓa”.

“Za a iya bayyana sunayensu ga jama’a kan abin da suka yi”.

“Kazalika, laifi ne a samu ɗan majalisa da hannu a wata badaƙala ƙarkashin sashe na 24 na ‘dokar ɗa’ar ma’aikata’ ta ‘yan majalisar”.

Wani tsohon Kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na’abba ya ce “idan har akwai zarge-zarge kan mambobin majalisa, kamata ya yi kwamitin ɗa’a ya yi bincike”.

Idan har zarge-zargen gaskiya ne, sai a miƙa waɗanda suka yi laifin hannun hukumomin da abin ya shafa domin su fuskanci tuhuma”

..

Duk da rashin jituwar da aka samu tsakanin jami’an hukumar NDDC da majalisar dokokin Najeriya, Shugaba Buhari ya gargaɗi ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da kada su nuna ‘rashin girmamawa’ ko yi wa majalisar ‘maƙarƙashiya’.

Shugaban ya ɗan sa baki yayin wani taro da shugabannin majalisun ƙasar.

Zuwa yanzu, za a ci gaba da bincike yayin da ‘yan Najeriya ke dakon ganin yadda binciken badaƙalar kuɗin naira biliyan 81 a hukumar NDDC da aka ƙirƙireta domin magance matsalolin da al’ummar yankin Neja Delta mai arzikin mai ke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: