Covid-19: Akwai Jami’an Kiwon Lafiya 14 Dauke Da Korona A Yobe.

0
257

Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

KWAMISHINAN ma’aikatar kiwon lafiya a jihar Yobe, Dr. Muhammad Gana ya ce akwai jami’an kiwon lafiya kimanin 14 da ke aikin yaki da yaduwar annobar korona a jihar Yobe, su na daga cikin jimlar mutum 62 wadanda gwajin kwayar cutar ya nuna sun kamu da cutar.
 Dr. Gana ya Kara da cewa mutum 62 da aka tabbatar su na dauke da cutar, su na daga cikin adadin mutane 229 wadanda kwamitin yaki da yaduwar cutar korona a jihar Yobe ya gudanar wajen aikin gwaje-gwajen jama’a domin tantance ma su kwayar cutar.
Kwamishinan, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin yaki da yaduwar annobar Korona, wanda Daraktan kula da ma’aikatan jinya a ma’aikatar kiwon lafiya- Abdullahi Danchuwa ya wakilta, ya sake bayyana cewa kimanin mutane 51 da su ka harbu da kwayar cutar, wadanda aka killace a cibiyoyin kula da ma su cutar a jihar, sun wartsake kuma kawowa yanzu an sallame su.
Dr. Gana ya bayyana hakan ne a wani shirin wayar da kan jama’a dangane da cutar, a karamar hukumar Gujba, inda ya gana da sarakunan gargajiya da shugabanin addini a yankin, tare da tattauna muhimman al’amurra kan cutar korona.
Ya ce mutum takwas kwayar cutar ta kashe a fadin jihar Yobe.
Kwamishinan ya Kara da cewa, wannan adadi na mutanen da annobar korona ta kama sun fito ne daga kananan hukumomin 13 da ke jihar; akwai mutane 22 a Damaturu, sai Nguru mutane15, Bade (Gashu’a) 13, Potiskum Kuma 3, yayin da kananan
hukumomin Geidam, Karasuwa, Yusufari, Tarmuwa, Bursari, Fika, Fune, Gulani da Gujba, kowace ta na da mutum daya dake dauke da wanna cutar ta Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here