Gobarar Tankar Mai Ta Kashe Mutane 20 A Delta

0
270
Rabo Haladu Daga Kaduna
MUTANE akalla 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta da wata tankar mai tayi a yankin Niger Delta.
Lamarin ya faru a ranar Laraba a kan babbar hanyar da ke haɗa jihar Edo da kuma jihar Delta.
Wasu daga cikin mutanen sun ƙone ƙurmus yadda ba za a iya gane su ba.
Ganau sun bayyana cewa galibin waɗanda suka mutu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke ƙokarin ɗiban mai daga tirelar wacce ta faɗi.
Take wuta ta tashi kuma ta fantsama a kan hanyar ta kuma kama wasu daga cikin motocin da ke wucewa a kan hanyar.
Wani jami’in gwamnatin jihar Delta ya shaida wa manema labarai  cewa tirelar ta kife ne a lokacin da take kokarin shan wata kwana sannan daga bisani ta kama da wuta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here