Marigayi Isma’ila Isa Aminina Ne – Balarabe Musa

0
307
Marigayi Sama'ila Isa Funtuwa da Abba Kyari duk aminan Mamman Daura ne...
Mustapha Imrana Abdullahi
TSOHON Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Abdulkarir Balarabe Musa ya bayyana marigayi Malam Isma’ila Isa Funtuwa a matsayin amininsa da suka dade suna hulda tun suna yara.
Balarabe Musa ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da kafar yada Labaran rediyon Jihar kaduna ta KSMC inda ya ce hakika suna tare da marigayin tare da yayansa marigayi Alhaji Mu’azu Isa Funtuwa.
Balarabe Musa ya ci gaba da cewa ” Duk da Isma’ila Isa ya kasance dan Jam’iyyar NPN ne a lokacin da na yi takarar Gwamna a tsohuwar Jihar Kaduna, marigayi Isma’ila Isa ya fito fili ya nuna mini goyon baya har Allah yasa na samu nasarar lashe zaben Gwamnan a karkashin jam’iyyar PRP na zama Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna”. Inji Balarabe Musa.
Ya kara da cewa hakika an yi babban rashi a kasa baki daya, don haka muna yin addu’ar Allah ya gafarta wa marigayi Isma’ila Isa Funtuwa ya albarkaci abin da ya bari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here