Ranar Juma’a Ta Sama Za A Yi Babbar Sallah A Najeriya – Sarkin Musulmi

0
373
Mai alafarma Sarkin Musulmin Najeriya
Rabo Haladu Daga Kaduna
KWAMITIN ganin wata da ke karkashin shugabancin Sarkin Musulmi na Najeriya ya ce ranar Juma’a 31 ga watan Yuli za a gudanar da Idin Babbar Sallah.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kamitin ya ce an ga sabon watan Dhul Hijjah a wurare da dama na kasar nan ranar Talata, don haka Laraba ce daya daga watan Dhul Hijjah.
A cewarsa, an ga sabon watan ne a Abuja da Jalingo da Ilorin da Lafiya da Minna da kuma Misau.
Ya kara da cewa masarauta Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III za ta fitar da sanarwa a hukumance da za ta yi cikakken bayani kan tsarin Babbar Sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here