Dakta Shinkafi Ya Soki Nadin Sarautar Da Aka Yi Wa Femi Fani Kayode

0
232
Mustapha Imrana Abdullahi
DOKTA Suleiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi ya bayyana rashin gamsuwa da nadin sarautar da Sark8n Shinkafi ya yi wa Mista Femi Fani Kayode.
Dakta Suleiman Shu’aibu  Shinlafi ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira, inda ya ce hakika abin da Sarkin ya yi na Nada wa Femi Fani Kayode Sarautar gargajiya da sunan masarautar Shinkafi sam ya saba wa tsarin mutunci da Martabar mutanen masarautar baki daya.
“Ta yaya za a nada mutumin da bai san mutuncin mutanen arewacin Nijeriya ba? Yana zagin yan Arewa a duk lokacin da ya ga dama har a jaridu da sauran kafafen yada labarai da shafukansa na zumunta amma haka kawai a zauna a cikin otal ace wai an ba irin wannan mutum Sarauta.
Ya ci gaba da cewa ba a tuntubi kowa ba haka kawai ba bin  tsarin da ya dace don kawai akwai wata bukatar da mutanen da suka yi wannan ABU su suka san dalilin.
” Daga yau na ajiye Sarauta ta ta Sarkin Shanun Shinkafi kuma da akwai wani Malamin jami’a a Sakkwato shima ya ajiye tasa Sarautar da masarautar Shinkafi ta bashi”.
Ya kara da cewa ” Ni a Shinkafi aka haife ni amma ban san wani lokacin da Femi Fani Kayode ya taba Alakanta kansa da mutanen masarautar Shinkafi ba, kuma ban san lokacin da ya zo domin yin wani abin da zai taimaki jama’ar Jihar Zamfara ba, kullum wannan mutum aikinsa cin mutunci da zagin Arewa da mutanen ta saboda haka a kan wace hujja za a bashi Sarauta da sunan Shinkafi.
Kuma “ni zan ta fi kotu domin in kalubalanci wannan tsarin bayar da sarauta da ya yi kama da kwadayin abin duniya”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here