Matasa Kimanin Dubu 5 ne A Yobe Suka Amfana Da Tallafin Kayayyakin Sana’o’in Hannu Na Naira Miliyan 114 .

0
363
Muhammad Sani Gazas Chinade , Daga Damaturu
GWAMNA Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kashe kimanin naira miliyan 114 wajen raba wa matasan da su ka samu horon bunkasa kananon sana’o’in hannu dabam-dabam, ta hadin gwiwa da shirin cimma muradun karni (SDG) dake Jihar.
Buni ya bayyana hakanne yayin da yake rantsar da kwamitin gudanar da hukumar kyautata walwalar jama’a da jin dadin su, a garin Damaturu wadda mataimakin sa, Alhaji Idi Barde Gubana zai jagoranta.
Ya Kara da cewa, shirin wani bangare ne na gwamnatin jihar wajen kokarin kirkiro da ayyukan yi da yaki da talauci.
Gwamna Buni wanda mataimakin sa Idi Gubana ya wakilta a taron, ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta samar da filayen noma kimanin kadada 500 domin raba su ga matasa 5,000 a shirin noman rani.
Ya kara da cewa, filayen noman wadanda su ke a yankunan Jakusko, Boloram, Mugura da Nguru, za a yi amfani da su ne domin matasan saboda bunkasa noma kayan abinci.
Har Ila yau kuma Gwamna Buni ya ce a yan kwanakin nan, gwamnatin jihar ta ware filayen noman damina kimanin kadada 1,000, ingantattun iraruwa, da takin zamani kyauta ga matasa a Damaturu, a karkashin shirin  bunkasa noma ga matasa.“Haka kuma mu tsara sayan amfanin gonar da matasan su ka noma tare da amfani da shi wajen habaka ingantattun iraruwa ta hadin gwiwa da hukumar samar da ingantattun iraruwa ta Nijeriya.” In ji shi.
A cewarsa, “Shirin kyautata walwalar jama’a da jin dadin su, hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya, hadi da kungiyoyin agaji da ci gaba, don hada hannu waje guda a yaki talauci da zaman kashe wando da al’umma ke fama da shi”
Gwamnan ya kawo wasu daga cikin ayyukan kwamitin wadanda su ka hada da sanya ido tare da auna yadda abubuwa ke gudana, bibiyar tsare-tsaren yadda kungiyoyin ke tafiyar da ayyukan su wajen tallafa wa rayuwar al’ummar jihar, da makamantan haka.A nasa jawabin a wajen taron, wakilin kungiyar ‘Save the Children’, Mista Atiku Yola, ya sanar da cewa kungiyarsu ta na ci gaba da tallafa wa al’ummar jihar a kokarin ta wajen rage radadin matsalar tsaron Boko Haram suka haifar.
Ya kara da cewar kimanin kananan yara 10,000 ke karbar tallafin naira 5,000 a kowane wata, wanda aka shafe akalla watanni 33 ana gudanar da shi a wasu sassan jihar ta Borno.
Har ila yau kungiyar su ta taimaka wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiya, wajen samun kwarewa kan yadda za su fuskanci matsalolin karancin abinci mai gina jiki da mafi yawan yaran yankin ke fuskanta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here