‘Yan Bindiga Sun Saki Fursunoni A Barikin Ladi Bayan Kai Hari

0
234
Daga Usman Nasidi.
RAHOTANNIN da ke shigowa sun tabbatar da cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an tsaron gidan yari a Barikin Ladi, sun aikata mummunar ta’asa.
Rahotannin sun bayyana cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an tsaron gidan kurkuku a Barikin Ladi da ke jihar Filato, inda suka saki fursunoni.
‘Yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne, sun kai hari kan ayarin jami’an hukumar gidajen gyara hali a kusa da Babbar Kotun Filato da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi, inda suka ‘yantar da masu laifi shida.
Rahotanni sun bayyana cewa, harin na kwanton bauna ya auku ne a yayin da ake jigilar wasu mutane 14 da ake zargi da laifuka daban-daban kama daga kisan kai, garkuwa da mutane da kuma fyade.
Wani mutum da shaidi aukuwar wannan lamari, ya ce ayarin bayan isowarsa harabar Kotun, ‘yan bindigar da suka noke a bakin Kotun, suka bude wuta tare da sakin fursunoni ba tare da an iya mayar musu da martani ba.
Kwamandan hukumar tsaron gidajen kaso na jihar Filato, Mista S. A Musa, ya ce kotun ba ta sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan jihar ba, Edward Egbuka, cewa an sauya ranar sauraron karar masu laifin.
Sai dai jami’an ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wasu mutum da ke zargi da aikata wannan laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here