Zulum Ya Razana Da kisan Gillar Ma’aikatan Agaji 5 A Borno.

0
298
Sani Gazas Chinade, Damaturu

GWAMNA Farfesa Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya bayyana kaduwa da razanarsa dangane da kashe ma’aikatan bayar da agajin gaggawa 5 da mayakan Boko Haram su ka aiwatar, bayan sun yi garkuwa da su a makonnin Baya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun babban mai taimaka masa a harkokin yada labarai da tsare-tsare, Malam Isa Gusau. Inda ya nuna matukar bacin ransa, tare da bayyana ma’aikatan a matsayin “gwarzayan hidimta wa al’umma”.

Malam Isa Gusau ya kara da cewa, Gwamna Zulum ya samu wannan mummunan labarin da yammacin ranar Laraba, a sa’ilin da yake ziyara a shalkwatar jami’an tsaron jar-kwala na Nijeriya, a birnin tarayya na Abuja domin tattauna lamurran da su ka shafi tsaro dangane da jihar ta Borno.

“Wanda a cikin wani faifan bidiyo mayakan su ka nuna ma’aikatan su biyar tare da zartas mu su da hukuncin kisa, ta hanyar umurnin wani daga cikin kwamandojin maharan.”

“Wadannan ma’aikatan Agajin dai an sace su ne a makonin da su ka gabata, a daidai lokacin da su ke gudanar da ayyukan jinkai ga dubban ‘yan gudun hijira.”

Ya kara da cewa, “Gwamna Zulum ya yi matukar nuna bacin ransa tare da bayyana razanar sa kan wannan kisan gilla ga wadannan ma’aikatan agajin gaggawa, wadanda su ka rasa rayukan su a aikin jinkai ga ‘yan gudun hijira.”

Don haka Gwamna Zulum ya mika sakon ta’aziyya da jaje ga ‘yan uwa da kungiyoyin da su ke yi wa aiki: hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA), kungiyar Action Against Hunger, Reach International, International Rescue Committee, tare da ofishin ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya a Nijeriya (UNOCHA).” kwata.

Isa Gusau ya sanar da cewa, duk da kasancewa Gwamna Zulum a wannan lokaci, ya tura manyan jami’an gwamnatin sa wajen halartar jana’izar ma’aikatan tare da jajantawa iyalan Mamatan.

A cewarsa Gwamna Zulum ya na kokarin fito da wasu sababbin matakan da za su taimaka wajen kawo karshen wadannan kashe-kashen babu gaira ba sabar a jihar.

Ya ci gaba  da cewa ba zai yuwu ba a zuba ido irin wadannan abubuwa su na abkuwa a kai-a kai ba tare da taka musu birki kan wannan aika-aika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here