Ba Mu Taba Ganin Rashin Cinikin Raguna Irin Na Bana Ba-Kawu Muhammad 

  0
  561
  Wani rago da aka saya kan kudi N120,000 a kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos

  Isah Ahmed Daga  Jos

  SHUGABAN kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Kawu Muhammad ya bayyana cewa basu taba ganin rashin cinikin raguna a kasuwarsu, irin na bana ba. Alhaji Kawu Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, kan  harkokin kasuwancin sayar da raguna a shirye shiryen sallar idin layya ta bana.

  Ya ce a bana dai irin halin  da suka shiga, sai dai su yiwa Allah godiya, kan rashin cinikin raguna. Domin a baya  idan irin wannan lokaci yazo, musulmi masu karfi har da wadanda ba musulmi ba,  suna zuwa su sayi raguna su rabawa jama’a,  amma bana abin ba haka yake ba.

   

  • Wasu raguna a kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos
  • Wasu raguna a kasuwar dabbobi ta Nasarawa da ke garin Jos

   

   ‘’A bana kowanne irin kala na rago  akwai su a wannan kasuwa, babba da karami tun daga farashin N12,000 zuwa N15,000 zuwa N25,000 zuwa N35,000 zuwa 45,000 zuwa N55,000 zuwa N150,000  duk akwai su. Amma ga su nan babu mutane,  don haka babu ciniki  saboda halin da muka shiga na wannan  annoba ta Kurona’’.

  Alhaji Kawu ya yi bayanin cewa  garin   Jos kamar wata cibiya  ce, domin akwai masu zuwa kasuwar daga Legas, Abekuta,  Ibadan,  Fatakwal, da dai sauransu da suke   zuwa su sayi raguna  su tafi da su,  amma bana abin ya gagara  kowa sai ya ce babu kudi.

  Ya ce bana  mutane ba sa maganar yin layya, sai dai maganar yadda za a ciyar da yara da sauran iyalai.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here