Hana Shigo Da Masara Daga Waje Ya Yi Wa Manoma Dadi

0
556
Sai shuka kenan!

 Isah  Ahmed Daga  Jos

MANOMAN masara a Najeriya, sun yi farin ciki da matakin da babban bankin Najeriya (CBN) ya dauka, na dakatar da shigo da masara daga wajen Najeriya.

Shi dai babban bankin na Najeriya [CBN] ya bayyana dakatar da shigo da masarar  ce, ta hanyar bayyana daina bayar da canjin musayar kudaden waje, ga masu sayo masara daga kasahen waje, a makon da ya gabata.

  • Alhaji Dayyabu Hussaini Ramin Kura
  • Alhaji Tasi’u Bako Nabawa.

A zantawarsa da wakilinmu kan wannan al’amari, wani manomin masara a yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna, yankin da yafi kowanne yanki noman   noman masara a Najeriya, kuma shugaban kungiyar noma don riba na garin Saminka. Alhaji Tasi’u Bako Nabawa ya bayyana cewa babu shakka suna  maraba da  wannan mataki, da gwamnati ta dauka na hana shigo da masara, daga waje.

Ya ce shigo da masara daga wajen Najeriya, wata kutungula ce da abokan zamanmu suke kullawa.

  • Alhaji Umar Liman Doka.

Ya ce a baya  an wayi gari ana sayar da buhun masara kan kudi N6,000 saboda shigo da masarar da ake yi daga waje.

Ya ce idan muka dubi hana shigo da shinkafa kasar nan da aka yi, an sami gagarumin cigaba, domin ga kamfanonin sarrafa shinkafa ‘yar gida nan, suna ta bunkasa.

Ya ce don haka wannan mataki, zai taimaka  wajen bunkana noman masara a Najeriya.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, wani manomin masara Alhaji Dayyabu Hussaini Ramin Kura, cewa ya yi a matsayinsa na manomin masara, yaji dadin daukar wannan mataki da gwamnati tayi. Domin   zai  kara karfin gwiwa ga manoman masara. kuma zai taimakawa kasar nan, wajen samar da aiki ga matasa, da samar da wadatatcen abinci.

Ya ce babu shakka shigo da masara daga waje, ya kawo karyewar manoman masara da dama a Najeriya. Don haka wannan mataki ya yi daidai, domin zai farfado da manoman masara, kuma zai bunkasa noman masarar a kasar nan.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, wani manomin masara Alhaji Umar Liman Doka, ya ce  tsakani da Allah, sun yi farin ciki da wannan mataki da gwamnati ta dauka.

Ya ce dama su manoman masara, musamman manoman masara na wannan yanki, abin da suke nema ke nan, domin kowa ya sani  Najeriya baki daya, karamar hukumar Lere ce kan gaba wajen noman masara.

Ya ce  idan sun noma masara a baya, suna sayar da buhu kan N6,000 saboda   cushewar da take yi a kasuwanni,  saboda shigo da ita da ake yi daga waje.

Ya ce amma yanzu sun gode wa  Allah, da  gwamnati ta dauki wannan mataki, na hana shigo da masara daga waje, kamar yadda ta hana shigo da shinkafa.

‘’Muna kira ga shugaban kasa ya dada bunkasa  aikin noma a Najeriya, domin kamar yadda duniya ta shiga annobar Kurona, da a ce bamu shiga noman shinkafa ba, ba zamu iya tafita kasashen waje, don shigo da  shinkafar ba. Don haka idan aka bunkasa noman masarar nan, zamu iya noma marasa da za mu  ci mu bai wa makotanmu’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here