Kwanaki 10 Na Watan Zhulhijah Suna Da Mahimmanci Ga Musulmi-Sheikh Jingir

  0
  377

  Isah Ahmed Daga  Jos

  SHEIKH Muhammad Sani Yahya Jingir, shi ne Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ,ya bayyana mahimmanci kwanaki 10 na farkon watan Zhulhijah, ga al’ummar musulmi da abubuwan da ya kamata  su yi a cikin wadannan kwanaki. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Ganin irin mahimmancin   kwanakin 10 na farko na  watan nan na  Zhulhijah da ya kama  ga al’ummar musulmi, mene ne ya kamata suyi  a cikin wadannan kwanaki?

  Sheikh Jingir: Babu shakka wadannan kwanaki 10 na farkon watan Zhulhijah, suna da matukar mahimmanci ga al’ummar musulmi. Don haka akwai ayyuka da dama na samun lada, da suka kamata musulmi ya yi.

  Malaman tafsiri sun ce tun daga ranar 1 ga watan na Zhulhijah, har zuwa ranar sallah wato ranar 10 ga watan.  Akwai azumi na nafila a cikin kwanaki 9 na  wadannan kwanaki. Wato tun daga ranar 1 ga watan, har zuwa ranar 8 ga watan, mutum zai iya yin wannan azumi na nafiya, idan yana son ya yi.

  Sannan kuma ranar 9 ga watan, shi ne ranar arfa. Don haka wanda ya sami ikon zuwa aikin hajji, a wannan rana zai yi hawan arfa. Kuma  a wannan rana, babu alhazai a cikin wannan azumi.

   Wanda bai sami damar zuwa aikin hajji ba.  sunnah ce ta Manzon Allah SAW ya yi azumi a ranar arfa.  Manzon Allah SAW ya ce wanda ya yi azumin ranar arfa, za a yaye masa zunubansa na bara, da zunubansa na shekara mai zuwa.

  Washe gari kuma wata ranar 10 ga wata, shi ne ranar sallar idin layya wato a wannan rana ce ake yanka layya.

  GTK:To,  yaya ake yin wannan layya?

  Sheikh Jingir: To, ita dai layya ana yin ta ne bayan an sauko daga idi.  kuma sai liman ya yanka, sannan ne mamu zasu yanka. Duk wanda ya riga liman yanka abin layyarsa, layyarsa ba ta yi ba. Domin a tsarin musulunci akwai girmama shugabanci.

   Kuma ba a yin babbar sallah sai an sauka daga arfa. Domin a tsarin musulunci ranar arfa daban, ranar babbar sallah daban daban.

  Idan aka sauko daga sallar idi, sai kowa ya yanka layyarsa. Kuma jama’ar musulmi ban da rowa, idan da hali ayi layya. Kuma bayan mutum ya yanka layyarsa, idan yana da hali ya yankawa mahaifansa. Amma a addinin musulunci sai mutum ya fara yanka tasa layyar, kafin ya yankawa mahaifansa da iyalansa.

  GTK: Wadanne irin dabbobi ne ake yin layya da su?

  Sheikh Jingir: Dabbar layyar  ta gaba shi ne rago, mai kahonni fari, ko kuma tunkiya. Kuma ba a yanka mai ido daya ko gurgu ko ramamme mara mai.

  Bayan rago sai awaki kamar bunsuru wanda aka dandake da wanda ba a dandake ba, ko kuma   akuya. Daga nan sai  sa, namiji  da ke ko dandakake, sai saniya. Daga nan kuma, sai rakumi ko taguwa.

  Kuma ita layya ana lura da dadin nama ne, don haka aka ce rago  ne kan gaba, domin   naman rago yafi sauran da suka biyo baya dadi.

  Amma idan hadaya ce wadda ake yi a lokacin aikin hajji, yawan nama aka fi so. Don haka aka ce a  yanka rakumi ko sa.

  GTK: mene ne ya kamata mai niyar yin layya, ya yi a cikin wadannan kwanaki?

  Sheikh Jingir: Duk wanda ya shiga aikin hajji, ba zai yi  aski ba, ba zai yanke farce ba, kuma ba zai yi qaho ba. Mu kuma a gida ga wanda bai sami tafiya aikin hajji ba, amma Allah ya hore masa zai yi layya, kada  ya yanke farcensa kada ya aske kansa, kada ya yi gyaran fuska. Tun daga ranar 1 ga watan Zhulhijah har sai an je an sauko daga masallacin idi,  ya zo ya yanka layyarsa.

  GTK: Mene ne  ya kamata musulmi  suyi a ranar sallah?

  Sheikh Jingir: Abin da ya kamata musulmi su yi a ranar sallah shi ne su yi  wanka su yi ado su sanya kaya masu kyau, su sanya turare su  tafi masallacin idi. Abi hanya idan za a dawo a koma ta wata hanyar. Ana tafiya ana cewa Allahu Akbar La’ila ha’ilallah Walillahil hamdu. Kuma idan mutum zai iya, an fi so ya tafi da kafarsa,  a tafi  cikin natsuwa.

   Idan an dawo a zo a ci abinci a bai wa makota, a raba naman layya ga al’ummar musulmi da wadanda ma ba musulmi ba. Domin mahimmancin zaman lafiya a tsakani. Kuma babu zage zage, sannan kuma a yabawa mata da suke aikin girke girke a cikin gidajenmu. Sannan kuma a zo a yi wa juna barka da sallah, duk wadannan abubawa ne da ake son a yi su a wannan rana.

  Kuma kada samari, saurayi da budurwa  su debi jiki su tafi yawo gidan zoo, ko kuma wasu wurare da ba su dace ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here